Ga yadda abubuwa duka suka kasance, tun daga farko. Allah ya hallaci sammai da dukan abubuwan da ke cikin su chikin kwana shida. Bayan Allah ya hallaci duniya, duhu ya maimaye ta, cikinta kuma wofi ne, ba a kuwa hallici kome ba. Amma Ruhun Allah yana nan bisa ruwa.
Sa'annan Allah ya ce, "Bari haske ya kasance!" Sai haske ya kasance. Allah ya ga hasken yana da kyau, ya kira shi "yini". Ya raba shi daga duhu wanda ya kira "dare." Allah ya hallaci haske a rana ta fari na halitta.
A rana ta biyu ta halitta, Allah ya yi magana ya hallici sarari bisa duniya. Ya yi sarari ta wurin raba ruwan sama daga ruwan kasa.
A rana ta ukum Allah ya yi magana ya raba ruwa daga busasshiyar kasa. Ya kira busasshiyar kasar "duniya," ya kuma kira ruwan, "tekuna." Allah ya ga abinda ya halitta yana da kyau.
Sa'annan Allah ya ce, "Bari kasa ta fitar da itatuwa iri iri da tsire tsire." Haka kuma ya faru. Allah ya ga abinda ya halitta yana da kyau.
A rana ta hudu na halitta, Allah ya yi magana, ya yi rana da wata da kuma taurari. Allah ya sa su, su ba da haske bisa duniya, su kuma raba yini da dare, lokatai da shekaru. Allah ya ga abinda ya halitta yana da kyau.
A rana ta biyar, Allah ya yi magana, ya yi dukkan abubuwan dake fitto a ruwa da dukkan tsuntsaye. Allah ya ga yana da kyau, ya kuma albarkace su.
A rana ta shida na halitta, Allah ya ce, "Bari kowanne irin dabbobin kasa su kasance!'' Sai ya faru kamar yadda Allah ya fada. Wadansu dabbobin gida ne, wadansu kuma masu rarrafe ne a kasa, wadansu kuwa dabbobin jeji ne. Sai Allah ya ga yana da kyau.
Sa'annan Allah ya ce, "Bari mu yi mutane cikin surarmu, su zama kamarmu. Za su zama da iko bisa duniya da dukan dabbobi."
Sai Allah ya dibi kasa, ya siffanta shi mutum, ya kuma hura rai a cikinsa. Sunan mutumin nan Adamu ne. Allah ya dasa gona inda Adamu zai iya zama, ya ajiye shi a wurin ya lura da ita.
A tsakiyar gonar, Allah ya dasa itatuwa biyu na musamman- itacen rai da itacen sanin nagarta da mugunta. Allah ya gaya wa Adamu zai iya ci daga kowanne itace da ke gonar, amma banda itacen sanin nagarta da mugunta. Idan ya ci daga wannan itacen, zai mutu.
Sa'annan Allah ya ce, "Bai kyautu mutum ya kasance shi kadai ba." Amma babu ko daya daga cikin dabbobin da zai iya zama mataimakin Adamu.
Sai Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zuryi. Sa'annan Allah ya dauki daya daga cikin hakarkarin Adamu ya maida shi mace ya kawo masa ita.
Da Adamu ya ganta, ya ce, "Hakika! Wannan ta yi kama da ni! Bari a kirata 'Mace,' domin an yi ta daga Namiji." Shi yasa namiji ke barin mahaifinsa da mahaifiyarsa ya zama daya da matarsa.
Allah ya yi namiji da ta mace cikin surarsa. Ya albarkacesu ya ce masu, "Ku haifi 'ya'ya da yawa da jikoki ku cika duniya!" Allah ya ga dukan abubuwan da ya yi suna da kyau kwarai, ya kuma gamsu da dukansu. Duk wannan ya faru a rana ta shida na halitta.
A rana ta bakwai, Allah ya gama aikinsa. Sai Allah ya huta daga dukkan abinda yake yi. Ya albarkaci rana ta bakwai, ya kebeta da tsarki, domin a ranar ne, ya huta daga aikinsa. Haka Allah ya hallici duniya da sammai da dukkan abubuwan dake cikinsu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 1- 2
Adamu da matarsa kuwa suna rayuwa cikin farin ciki, a kyakkyawar gonar da Allah ya yi masu. Babu wanda ke sanye da tufafi a cikin su, amma duk da haka basu ji kunya ba domin babu zunubi a duniya. Sau dayawa sukan yi tafiya tare da Allah suna kuma magana da shi.
Amma akwai wani mayaudarin maciji cikin gonar. Ya tambayi matar, ''Ko da gaske ne Allah ya gaya maku kada ku ci, 'ya'yan wani itace daga itatuwan da ke gonar?''
Sai matar ta amsa, "Allah ya ce mana zamu iya cin ya'yan kowanne itace amma banda na itacen sanin nagarta da mugunta. Allah ya fada mana, 'Idan kuka ci 'ya'yan itacen, ko kuka taba shi, zaku mutu."'
Macijin ya amsa wa matar, "Wannan ba gaskiya ba ne! Ba zaku mutu ba. Allah dai ya san cewa da zarar kun ci ya'yan itacen, zaku zama kamar Allah zaku kuma san nagarta da mugunta kamar yadda ya sani.''
Matar ta ga 'ya'yan itacen na da kyau da kuma bansha'awa. Tana kuma so ta zama mai hikima, sai ta tsinki wassu 'ya'yan itacen ta ci. Sai ta ba wa mijinta, wanda ke tare da ita, shi ma ya ci.
Nan take sai idanun su suka bude, suka gane tsirara suke. Suka yi kokarin rufe jikunan su, ta wurin dinka ganyaye domin suyi tufafi.
Sa'annan mutumin da matarsa suka ji motsin Allah yana tafiya a gonar. Sai dukkan su suka boye wa Allah. Sai Allah ya kira mutumin, "Ina kake?'' Adamu ya amsa, "Na ji tafiyarka a cikin gonar, na tsorata, domin tsirara na ke. Don haka na buya."
Sai Allah ya tambaye shi, "Wa ya gaya maka tsirara kake? Ko ka ci ya'yan itacen da na gaya maka kada ka ci?" Mutumin ya amsa, "Kai ka ba ni wannan mace, ita kuma ta ba ni 'ya'yan itacen." Allah kuma ya tambayi macen, "Me kenan ki ka yi?" Macen ta amsa, "Maciji ya yaudare ni."
Allah ya ce wa macijin, "An la'anta ka! Za ka yi tafiya rub da ciki, ka kuma ci kasa. Kai da macen za ku ki juna, sa'annan 'ya'yanka da ya'yanta zasu ki juna. Zuriyar macen zasu kuje kanka, kai kuma za ka yi wa diddigen sa rauni.
Allah kuma ya ce wa macen, "Zan sa haihuwa ta zama da zafi agareki. Muradin ki zai zama ga mijinki, shi kuma zai mallake ki.''
Allah ya ce wa mutumin, "Ka saurari matarka ka kuma yi mani rashin biyayya.Yanzu, an la'anta kasa, za ka kuma yi aiki tukuru, domin ka noma abinci. Sa'anan za ka mutu, jikin ka kuma zai koma turbaya.'' Mutumin ya kira matarsa Hawa'u, ma'ana, "mai bada rai," domin za ta zama uwa ga dukkan mutane. Sai Allah ya suturta Adamu da Hawa'u da fatun dabba.
Sai Allah yace, "Yanzu da 'yan Adam sun zama kamar mu, ta wurin sanin nagarta da mugunta, ba za'a yarda su ci 'ya'yan itacen rai su rayu har abada ba.'' Sai Allah ya kori Adamu da Hawa'u daga kyakyawar gonar. Allah ya sa mala'iku masu karfi a kofar gonar domin su hana duk wanda zai ci daga 'ya'yan itacen rai.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 3
Bayan tsawon lokaci, mutane da yawa suna rayuwa a cikin duniya. Suka zama mugaye masu husuma. Wannan kuwa yayi muni matuka, har Allah ya yanki shawara ya hallakar da dukkan duniya da gagarumar ambaliya.
Amma Nuhu ya sami tagomashi a wurin Allah. Shi mutum ne mai adalci, yana kuma zama cikin mugayen mutane. Allah ya gaya wa Nuhu game da ruwan tufanar da yake shirin aikowa. Ya gaya wa Nuhu ya gina babban jirgin ruwa.
Allah kuma ya gaya wa Nuhu ya gina jirgin da misalin tsawo kamu 140, fadi 23, tsayi kuma 13.5. Nuhu zai gina jirgin da katako, hawa uku da kuma dakuna ma su yawa, soro da kuma taga. Jirgin kuma zai dauki Nuhu da iyalinsa, da ko wane irin dabba dake fuskar kasa, sa'adda za'a yi ruwan tufana.
Nuhu ya yi biyayya da Allah. Shi da 'ya'yan sa uku suka gina jirgin kamar yadda Allah ya fada masu. Ginin jirgin kuwa ya dauki shakaru da yawa, saboda da girma sa. Nuhu kuma ya gargadi mutune game da ruwan tufana da ke zuwa, ya gaya masu su juyo ga Allah, amma basu gasganta shi ba.
Allah kuma ya umarci Nuhu da iyalinsa su yi tanadin abincin da zai ishe su, da kuma dabbobi. Sa'anda aka gama kome, sai Allah ya ce wa Nuhu lokaci yayi da shi, da matarsa, da 'ya'yansa uku da matan su, zasu shiga jirgin, mutane takwas kenan gaba daya.
Allah ya aiko namiji da tamace na kowane irin dabba da kuma tsutsu, wurin Nuhu domin su shiga jirgin su tsira lokacin da za'ayi ruwan tufana. Allah ya aiko maza bakwai da mata bakwai na kowane irin dabba da za'a iya amfani da su domin hadaya. Sa'adda dukka suka shiga jirgin, Sai Allah ya rufe kofar jirgin da kansa.
Sai aka fara ruwan sama, aka yi ta ruwa, aka yi ta ruwa. Aka yi ruwa yini arba'in da dare arba'in ba tsayawa! Ruwa kuma ya rika bubbugowa daga kasa a duniya. Ruwa kuma ya rufe kome dake cikin dukkan duniya, harma da tsaunuka da suka fi tsayi.
Dukkan abinda ke da rai a kan busasshiyar kasa ya mutu, saidai mutane da dabbobin dake cikin jirgin. Jirgin kuwa ya rika reto a kan ruwa, ya kuma tsirar da dukkan abinda ke cikinsa daga nutsewa.
Bayan da ruwan ya tsaya, jirgin yayi ta reto bisa ruwa na wata biyar, kuma a wannan lokacin ne ruwan ya fara janyewa. Watarana sai jirgin ya tsaya a kan wani dutse, amma duniya har yanzu tana mamaye da ruwa. Bayan karin watanni uku, sai saman tsaunuka suka bayyana.
Bayan karin kwana arba'in, sai Nuhu ya aiki tsuntsuwar da ake kira hankaka, domin ta ga ko ruwan ya janye. Amma hankakar ta yi ta firiya tana neman busashiyar kasa, ba ta samu ba.
Bayan haka Nuhu ya aiki tsuntsuwa da ake kira kurciya, ita ma bata sami busasshiyar kasa ba, sai ta dawo wurin Nuhu. Bayan mako guda ya sake aikan kurciyar, sai ta dawo da ganyen zaitun a bakinta! Ruwa ya fara janyewa, tsire-tsire kuma sun fara girma!
Nuhu ya sake jira mako guda sa'annan ya sake aikan kurciyar a karo na uku. A wannan lokacin kuwa ta sami wurin sauka, bata sake dawowa ba. Ruwan yana bushewa!
Bayan watanni biyu Allah ya ce wa Nuhu, ''Da kai da iyalinka da dukkan dabbobi zaku iya fita daga cikin jirgin yanzu. Ku haifi 'ya'ya da yawa da jikoki, ku kuma cika duniya.'' Sai Nuhu da iyalinsa suka fita daga jirgin.
Bayan Nuhu ya fita daga jirgin sai ya gina bagade, ya kuma yi hadaya da wassu daga cikin ire iren dabbobin da za'a iya yin hadaya da su. Allah kuma ya yi farinciki da hadayar, ya albarkaci Nuhu da iyalinsa.
Allah ya ce, ''Na yi alkawari ba zan sake la'anta kasa saboda miyagun ayyukan da mutane ke yi ba, ko in hallaka duniya ta wurin ruwan tufana, kodashike mutane masu zanubi ne tun lokacin da suke 'yan yara.''
Sa'annan ne Allah ya yi bakan gizo na fari, ya zama alamar alkawarinsa. A dukkan lokacin da bakan gizo ya bayyana a sararin sama, Allah zai tuna abinda yayi alkawari, haka kuma mutanensa.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 6-8
Shekaru da dama bayan ruwan tufana, mutane suka sake yawaita a duniya, kuma yare daya su ke yi. Maimakon su cika duniya kamar yadda Allah ya umarta, sai suka taru dukka suka gina birni.
Su na cike da girman kai, ba su kula da abin da Allah ya fada ba. Harma suka fara gina hasumiya mai tsawo da zai kai sama. Allah ya ga idan suka ci gaba da aiki tare domin aikata mugunta, zasu iya aikata wassu zunubai ma fiye da haka.
Saboda haka Allah ya sauya harshen su zuwa harsuna daban daban sai ya warwatsar da mutanen a dukkan duniya. Birnin da suka fara ginawa aka ce da shi Babila, ma'ana, "rudani."
Bayan shekaru aru-aru, Allah ya yi magana da wani mutum da ake kira Abram. Allah ya ce masa, "Ka bar kasar ka da iyalin ka ka je wurin da zan nuna maka. Zan albarkace ka in kuma maishe ka al'umma mai girma. Zan kasaita sunan ka. Zan albarkaci wadanda suka albarkace ka in kuma la'ananta wadanda suka la'ananta ka. Dukkan iyalan duniya za su sami albarka saboda kai."
Sai Abram ya yi biyayya da Allah. Ya dauki matarsa, Saraya, tare da dukan barorinsa da kuma duk abinda ya mallaka, ya tafi kasar da Allah ya nuna masa, kasar Kan'ana.
Sa'anda Abram ya iso Kan'ana, Allah ya ce, "Ka dubi kewayanka. Zan baka, da kai da zuri'arka iyakar kasar da ka iya gani a matsayin mallakar ka." Sa'an nan Abram ya zauna a kasar.
Wata rana, Abram ya sadu da Malkizadek, firist din Allah Madaukaki. Malkizadek kuwa ya albarkaci Abram ya ce, "Bari Allah Madaukaki wanda ke da sammai da duniya ya albarkaci Abram." Sa'an nan Abram ya ba wa Malkizadek daya bisa goma cikin dukkan mallakar sa.
Shekaru da yawa suka wuce, amma Abram da Saraya har yanzu basu sami 'da ba. Allah ya yi magana da Abram ya sake yin alkawari cewa zai sami 'da da kuma zuriya mai yawa kamar taurarin sama. Abram ya gaskanta alkawarin Allah. Allah kuwa yace, Abram mai adalci ne domin ya gaskanta da alkawarin Allah.
Sa'an nan Allah ya yi alkawari da Abram. Alkawari kuwa yarjejeniya ce tsakanin mutum biyu. Allah ya ce, ''Zan baka 'da daga jikin ka. Na bada kasar Kan'ana ga zuriyar ka.'' Amma har yanzu Abram ba shi da 'da.
Labari a Littafi Mai Tsarki: Daga Farawa 11-15
Bayan shekaru goma da isowar Abram da Saraya cikin Kan'ana, har yanzu basu sami 'da ba. Sai matar Abram, Saraya, ta ce masa, "Tunda Allah bai yarda mini in sami yara ba gashi yanzu na tsufa na kure don haihuwan 'ya'ya, ga baranya ta Hajaratu. Ka aureta domin ta haifi mani da.''
Sai Abram ya auri Hajaratu. Hajaratu ta haifi da namiji, Abram kuma ya bashi suna Isma'ilu. Amma Saratu yi kishin Hajaratu. Da Isma'ilu ya kai shekara 13, Allah ya sake magana da Abram.
Allah ya ce, " Ni ne Allah Mai Iko dukka. Zan yi alkawari da kai." Sai Abram ya yi ruku'u har kasa. Allah kuma ya ce wa Abram, "Zaka zama uban kabilu da yawa. Zan baka da zuriyarka kasar Kan'ana abin gado, kuma zan zama Allahnsu har abada. Dole ka yi wa kowane da namiji a iyalinka kaciya.''
Matarka, Saraya, zata sami da-zai zama dan alkawari. Ka bashi suna Ishaku. Zan yi alkawarina da shi, zai kuma zama babbar kabila. Zan maida Isma'ilu babban kabila kuma, amma alkawarina da Ishaku ne. Sai Allah ya sauya sunan Abram zuwa Ibrahim, ma'ana, "Uban masu yawa." Allah kuma ya sauya sunan Saraya zuwa Saratu, ma'ana, "gimbiya."
A wannan ranar Ibrahim ya yi wa duk mazajen da ke gidansa kaciya. Bayan shekara guda, sa'adda Ibrahim ya kai shekaru 100, Saratu kuma ta yi 90, Saratu ta haifa wa Ibrahim da. Suka bashi suna Ishaku kamar yadda Allah ya gaya masu su yi.
Sa'anda Ishaku ya ke dan saurayi, Allah ya gwada bangaskiyar Ibrahim da cewa, "Dauki Ishaku tilon danka ka kashe shi, ya zama hadaya a gareni." Sai kuma Ibrahim ya yi biyayya da Allah, ya shirya ya yi hadaya da 'dansa.
Sa'anda Ibrahim da Ishaku suke tafiya wurin hadaya, Ishaku ya yi tambaya, "Baba, muna da itace domin hadaya, amma ina dan ragon?'' Ibrahim ya amsa, "Allah zai tanada ragon hadaya, 'dana."
Da suka isa wurin hadaya, Ibrahim ya daure dansa Ishaku, ya kwantar da shi akan bagadi. Zai kashe dansa kenan, sai Allah ya ce, ''Dakata! Kada ka yi wa yaron rauni! Yanzu na san kana tsorona, domin baka hana mani danka tilo ba."
A kusa da wurin Ibrahim ya ga rago a sarkafe cikin daji. Allah ya riga ya tanada ragon hadaya amaimakon Ishaku. Da farin ciki Ibrahim ya mika ragon hadaya.
Sa'annan Allah ya ce wa Ibrahim, "Saboda ka amince ka bani kome, harma danka tilo, Na yi alkawari in albarkace ka. Zuriyarka zata fi taurarin sama yawa. Domin ka yi mani biyayya, dukkan iyalan duniya za su zama da albarka ta wurin iyalinka.''
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 16-22
Sa'anda Ibrahim ya tsufa sosai, 'dansa, Ishaku, kuwa ya girma ya kai namiji. Sai Ibrahim ya aiki daya daga cikin barorinsa, zuwa kasar da danginsa suke zama domin ya kawo wa dansa, Ishaku, mata.
Bayan tafiya mai nisa zuwa kasar da dangin Ibrahim suke zama, Allah ya bi da baran zuwa wurin Rifkatu. Ita jika ce ga dan'uwan Ibrahim.
Rifkatu kuwa ta yarda ta bar iyalin ta, ta koma tare da baran zuwa gidan Ishaku. Da isar ta kuwa Ishaku ya aure ta.
Bayan tsawon lokaci, Ibrahim ya mutu, sa'annan Allah ya mika wa Ishaku dukkan alkawaran da yayi masa cikin wa'adi. Alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim cewa zai sami iyalai da baza su kidayu ba, amma Rifkatu matar Ishaku bata iya samun 'ya'ya ba.
Sai Ishaku ya yi wa RIfkatu addu'a, Allah kuma ya yarda ta cikin tagwaye. Jariran biyu kuwa suka rika kokawa da juna tun suna cikin Rifkatu, sai Rifkatu ta tambayi Allah me ke faruwa.
Allah ya ce wa Rifkatu, ''Kabilu biyu zasu fito daga ''ya'ya biyun dake cikin ki. Zasu yi fama da juna, sa'annan babban dan zai bauta wa karamin.''
Sa'adda Rifkatu ta haifi 'ya'yan ta, sai babban 'dan ya fito ja da tsuma, sai aka sa masa suna Isuwa. Sai karamin 'dan ya fito yana rike da diddigen Isuwa, aka sa masa suna Yakubu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 24:1-25:26
Sa'anda yayan ke girma, Yakubu yana son zaman gida, amma, Isuwa yana son farauta, Rafkatu tana kaunar Yakubu amma Ishaku yana kaunar Isuwa.
Wata rana, da Isuwa ya dawo daga farauta, yana ji yunwa sosai. Sai ya ce wa Yakubu, "Ba ni daga cikin abincin da ka dafa." Sai Yakubu ya ce masa, "Da farko, ka ba ni matsayinka na dan fari." Sai Isuwa ya ba shi matsayinsa na dan fari. Sa'annan Yakubu ya ba shi abinci.
Ishaku ya so ya ba wa Isuwa albarkarsa. Amma kafin ya yi haka, Rifkatu da Yakubu suka yaudare shi ta wurin sa Yakubu ya badda kamaninsa, kamar shine Isuwa. Ishaku ya tsufa kuma baya ganin. saboda haka, Yakubu ya saka tufafin Isuwa, ya kuma daura fatar akuya a wuyarsa da hannayensa.
Yakubu ya zo wurin Ishaku, ya ce, "Ni ne Isuwa. Na zo domin ka albarkace ni." Da Ishaku ya taba gashin akuyar, ya sunsuna tufafin, sai ya yi tsammanin Isuwa ne, ya kuma albarkace shi.
Isuwa ya ki jinin Yakubu domin ya sace masa damar sa na dan fari, da kuma albarka. Sai ya yi niyyar ya kashe Yakubu bayan mutuwar mahaifinsu
Amma Rifkatu ta ji shirin Isuwa. Sai ita da Ishaku suka tura Yakubu wuri mai nisa, ya zauna da dangin ta.
Yakubu ya zauna da dangin Rifkatu shekaru masu yawa. A wannan lokacin, ya yi aure, ya haifi yaya maza goma sha biyu da ya mace guda daya, Allah ya azurta shi sosai.
Bayan shekaru ashirin da barin gidansa na kan'ana, Yakubu ya komo wurin da iyalinsa, da barorinsa, da dukkan garkin dabbobinsa.
Yakubu ya tsorata sosai domin yana tsamanin har yan zu Isuwa yana so ya kashe shi. Sai ya tura garkunan dabbobi masu yawa kyauta ga Isuwa. Barorin da suka kawo dabbobin suka ce wa Isuwa, "Bawan ka, Yakubu ne, ke baka wadannan dabbobin.Yana zuwa bada jimawa ba.
Amma Isuwa ya rigaya ya yafe wa Yakubu, sun yi murnar sake ganin juna. Sa'annan Yakubu yayi zaman salama a Kan'ana. Sai Ishaku ya rasu, Yakubu da Isuwa suka binne shi. Wa'din alkawaran da Allah ya yi wa Ibrahim ya ci gaba daga kan Ishaku zuwa kan Yakubu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 25:27-33:20
Bayan shekaru da yawa, a lokacin Yakubu ya tsufa, ya aika kaunataccan dan sa Yusufu ya duba yan'uwansa wadan da ke kula da garkuna.
'Yan'uwa Yusufu sun ki shi saboda mahaifinsu yafi kaunarsa kuma domin Yusufu yayi mafarki cewa, zai yi mulkinsu. Da Yusufu ya iso wurin 'yan'uwansa, suka kama shi kuma suka sayar da shi ga masu fataucin bayi.
Kafin 'yan'uwan Yusufu su koma gida, suka yage tufafin Yusufu suka tsoma shi cikin jinin akuya. Suka nuna wa mahifinsu tufafin Yusufu tufafiinsa domin ya yi tunanin cewa dabban daji ne ya kashe Yusufu. Yakubu yayi matukar bakin ciki.
Masu fataucin bayin kuwa suka kai Yusufu kasar Masar. Kasar masar kasa ce mai girma, da iko, kuma tana kusa da kogin Nilu. Masu fataucin bayin suka sayar da Yusufu bawa ga wani attajiri ma'aikacin gwamnati. Yusufu yayi wa mai gidansa bauta da kyau, Allah kuwa ya albarkace Yusufu.
Matar mai gidansa ta nemi ta yi zina da Yusufu, amma Yusufu ya ki yayi wa Allah zunubi ta wanan hanya. Matan ta husata sa'annan ta yi wa Yusufu zargin karya aka kama shi aka kai shi kurkuku. Ko acikin kurkuku, Yusufu ya cigaba da amincinsa ga Allah, Allah kuwa ya albarkace shi.
Bayan shakaru biyu, Yusufu na kurkuku, ko da shike shi ba mai laifi bane. A wata dare, Fir'auna, wanda shine yadda Masarawa ke kiran sarakunansu, ya yi mafarkai guda biyu da suka dame shi sosai. Ba wani a cikin mashawartansa da ya iya gaya masa ma'anar mafarkan.
Allah kuwa yayi wa Yusufu baiwan fassaran mafarkai, saboda haka Fir'auna ya aika a kawo masa Yusufu daga kurkuku. Yusufu ya fassara masa mafarkan cawa, "A cikin shekaru bakwai, Allah zai aiku yalwatacce girbi, bayan haka za'a yi shakaru bakwai na yunwa."
Yusufu ya burge Fir'auna har ya nada shi ya ya zama na biyu acikin wadanda suka fi iko a dukkan Masar.
Yusufu ya ce wa mutanen su yi ajiyan abinci da yawa a lokacin shakarun nan bakwai na kyakkyawan girbi. Sai Yusufu yana sayar da abinci ga mutane sa'anda shakaru bakwai na yunwa ya zo domin su sami isasshen abinci su ci.
Yunwan ta yi tsanani ba'a Masar kadai ba, amma har Kan'ana inda Yakubu da Iyalinsa suke zama.
Sai Yakubu ya aiki mayan 'ya'yansa maza zuwa Masar su sayo abinci. Yan'uwan ba su gane Yusufu ba yayin da suka tsaye a gabansa domin tsayen abinci. Amma Yusufu ya gane su.
Bayan ya gwada yan'uwansa ya gan ko sun canza, Yusufu ya ce masu, "Ni ne dan'uwan ku, Yusufu! Kada ku ji tsoro. Kun yi niyar yin mugunta sa'anda kuka sayar da ni bawa, amma Allah ya yi anfani da muguntar ya zama alheri! Ku zo ku zauna a Masar domin in tanada maku da Iyalanku."
Sa'anda yan'uwa Yusufu suka komo gida, suka fada wa mahifinsu, Yakubu, cewa Yusufu na da rai, ya yi faran ciki sosai.
Ko da shike Yakubu ya tsufa, ya tafi Masar da dukkan iyalansa, suka kuma zauna acan. Kafin mutuwan Yakubu, ya albarkaci kowane dansa.
Wa'adin alkawaran da Allah ya yi wa Ibrahim an mika wa Ishaku sa'annan ga Yakubu, da kuma 'ya'yan Yakubu goma sha biyu da iyalansu. Zuri'ar 'ya'ya goma sha biyun suka zama kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 37-50
Bayan mutuwar Yusufu, dukkan danginsa sun zauna a Masar. Su da zuri'arsu sun ci gaba da zama awurin shekaru da yawa, kuma suna da 'ya'ya masu yawa, ana kiran su Isra'ilawa.
Bayan shekaru aru-aru, yawan 'ya'yan Isra'ila ya karu sosai. Masarawa sun manta da Yusufu da dukkan aikin da yayi don taimakonsu. Sun ji tsoron Isra'ilawa domin yawansu. Sai Fir'auna da yake mulkin Masar a wannan lokaci ya maishe su bayi ga Massarawa.
Masarawa sun tilasta wa Isra'ilawa suyi gini-gine da yawa har su gina birane gabaki daya. Aiki mai wahalan sa rayuwarsu cikin takaici, amma Allah ya albakaci su, har sun sami karin 'yaya.
Fir'auna ya gani cewa Isra'ilawa suna samun jarirai da yawa, sai ya umurci mutanensa su kashe 'ya'ya maza jarirai ta wurin jefa su cikin Kogin Nilu.
Sai wata bayahudiya ta haifi da namiji. Ita da mijin sun suka boye jaririn iya kokarin su.
Da ya zama iyayen yaron baza su iya boye shi kuma ba, sai suka sa shi cikin Kwandon da baya nustewa tsakanin dogayen ciyayi da suke bakin Kogin Nilu domin su kare shi daga kisa. Baban yar'uwarsa tana kallo ta ga abinda zai faru da shi.
Wata 'yar Fir'auna ta ga Kwandon, ta dubi cikin. Da ta ga jaririn, ta dauke shi a masayin danta. Ta dauki wata bayahudiya yar aiki tayi renon sa ba tare sanin cewa matar mahaifiyar yaron bane. Sa'anda yaron ya kai yayewa, ta mayar da shi wurin 'yar Fir'auna, ta sa masa suna Musa.
Wata rana da Musa ya yi girma, sai ya ga wani bamasare yana dukan Ba-Isra'ile da ke bawa. Musa ya yi kokarin ceton dan'uwansa Ba-Isra'ile.
Musa ya yi tsammanin babu wanda zai gani, sai ya kashe Ba-Masaren ya kuma binne gawar. Amma wani ya ga abinda Musa ya yi.
Da Fir'auna ya ji abin da Musa ya yi, sai ya nemi ya kashe shi. Musa ya gudu daga Masar zuwa jeji inda zai tsere wa sojojin Fir'auna.
Musa ya zama makiyayi a jejin nesa daga Massar. Ya yi aure a nan matar ta haifa masa 'ya'ya maza biyu.
Wata rana, yayin da Musa na kula da tumakin sa, ya ga daji na ci da wuta. Amma dajin bata kone ba. Musa ya je gap da dajin domin ya gani da kyau. Da ya matso kusa da dajin da ke ci da wuta, muryar Allah ya ce, "Musa ka cire takalmanka. Kana tsaye a wuri Mai Tsarki."
Allah ya ce, "Na ga wahalar mutane na. Zan aike ka gun Fir'auna domin ka fitar da Isra'ilawa daga bautar su a Masar. Zan basu kasar Kan'ana. Kasar da na alkawarta wa, Ibrahim, Ishiyaka da Yakubu."
Musa ya yi tambaya, "Idan mutanen sun nemi sanin wanda ya aikoni, me zan ce?" Allah ya ce, "INA NAN YADDA NAKE. Ka gaya masu, 'NI NE ya aiko ni gare ku.' Ka kuma gaya masu, 'ni ne Yahweh, Allah na kakaninku, Ibrahim, Ishaku da Yakubu.' Wannan ne suna har abada."
Musa ya ji tsoro kuma baya so je wurin Fir'auna, domin ya yi tunani cewa, baya iya magana da kyau. sai Allah ya aiki dan'uwan Musa, Haruna, ya taimakeshi. Allah ya gargadi Musa da Haruna cewa Fir'auna ba zai saurare su ba.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Fitowa 1-4
Musa da Haruna sun je wurin Fir'auna. Suka ce, "Ga abinda Allah na Isra'ila ya ce, saki mutane na su tafi!" Fir'auna bai saurare su ba maimakon ya saki 'yayan Isra'ila su tafi, sai ya tilasta su suyi aiki mafi tsanani!
Fir'auna yayi ta kin barin mutanen su tafi, Sai Allah ya aiko da munana annoba guda goma a kan Masar. Ta wurin wandanan annoba, Allah ya nuna wa Fir'auna da allolin masar cewa ya fi su iko.
Allah ya mayar da kogin Nilo jini, Duk da haka Fir'auna bai saki Isra'ilawa su tafi ba.
Allah ya aiko da kwadi a dukan Masar. Fir'auna ya roki Musa ya kawar da kwadin. Amma bayan da duka kwadin sun mutu, Fir'auna ya taurare zuciyarsa kuma ya ki ya saki Isra'ilawa su bar Masar.
Saboda haka Allah ya aiko da annobar kwarkwata. Bayan haka sai Allah ya aiko da annobar kuda. Fir'auna ya kira Musa da Haruna ya fada masu idan sun tsayar da annobar, Isra'ilawa za su iya barin Masar. Da Musa ya yi adu'a, Allah ya kawar da dukan kudan daga Masar. Amma Fir'auna ya taurara zuciyarsa ya ki ya saki mutane su tafi.
Bayan haka, Allah ya sa duka dabbobin da a ke kiwo a gonakin Masarawa su kamu da cuta su mutu. Amma Fir'auna ya taurara zuciyarsa bai saki Isra'ilawa su tafi ba.
Sai Allah ya fada wa Musa ya watsa toka a iska a gaban Fir'auna. Da ya yi haka, sai marurai masu zafi sun fita akan Masarawa, amma ba a kan Isra'ilawa ba. Allah ya taurara zuciyar Fir'auna, kuma bai saki Isra'ilawan su tafi ba.
Bayan haka, Allah ya aiko da kankara da ya lalatar da mafi yawan amfanin gona da ke Masar ya kuma kashe duk wanda ya je wuje. Fir'auna ya kira Musa da Haruna ya kuma fada masu, "Na yi zunubi. za ku iya tafiya." Sai Musa ya yi adu'a, sa'annan kankaran ya daina fadowa daga sama.
Amma Fir'auna ya sake yin zunubi, ya kuma taurara zuciyarsa, ya ki ya saki Isra'ilawa su tafi.
Saboda haka Allah ya aiko da tarin fari su zo kan Masar. Wadannan farin sun cinye dukan amfani da kankaran bai lalatar ba.
Sai Allah ya aiko da duhun da ya dauki sawon kwana uku. Duhun yayi sanani har Masarawan ba su iya barin gidajensu. Amma a kwai haske a inda Isra'ilawa suke zama.
Ko bayan annoban nan tara, har yanzu Fir'auna ya ki ya saki Isra'ilawa su tafi. Tunda Fir'auna ya ki ji, Allah ya yi niyar aiko da annoba daya na karshe. Wannan zai sauya tananin Fir'auna.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Fitowa 5-10
Allah ya gargadi Fir'auna, cewa idan bai saki yayan Isra'ila su tafi ba, zai kashe dukan yan fari maza na mutane Masar da dabbobi. Da Fir'auna ya ji wannan, har yanzu ya ki ya gaskanta ya kuma yi biyaya da Allah.
Allah yayi tanadin hanyar ceton dan farin duk wanda ya gaskanta ga shi. Kowace iyali ta zabi dan rago mara lahani ta yanka
Allah ya fada wa Isra'ilawa su shafa jinin dan ragon kewaye da kofar gidansu, su gasa nama su ci agagauce tare da gurasa mara yisti. Ya kuma fada masu su shirya su bar Masar bayan sun ci
Israilawa sun yi komai kamar yadda Allah ya umurce su su yi. Da tsakar dare, Allah ya ratsa cikin Masar ya na kishan kowane dan fari.
Dukan gidajen Israilawa na shafe da jini kewaye da kofofin su, Allah ya ketare gidajen. Kowa da ke cikin su ya tsira. Sun tsira saboda jinin dan ragon
Amma Masarawa basu gaskanta Allah ko su yi biyaya da umuninsa ba. Don haka Allah bai ketare gidajensu ba, Allah ya kashe kowane daya na yayan fari maza na Masarawa.
Kowane dan fari na Masar ya mutu, daga dan farin wanda yake daure a kurkuku, zuwa dan farin Fir'auna. mutane da dama a Masar sun yi kuka da kururuwa saboda tsananin bakin ciki.
A wannan daren, Fir;auna ya kira Musa da Haruna ya ce, "Dauki Israilawa ku bar Masar nan take!" Mutanen Masar kwa suka roki Isra'ilawa su tafi nan take.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Fitowa 11:1-12:32
Isra'ilawa sun yi farin cikin barin Masar, sun fita daga bauta, sun kama hanya zuwa kasar alkawari! Masarawa sun ba su duk abin da suka tambaye su, har zinari, azurfa da kaya masu muhimminci, wadansu daga alummai sun gaskata da Allah, suka bi Isra'ilawa sa'anda suka fita daga Masar.
Allah ya bishe su da al'amudin girgije da ke gaban su da rana, wanda ya ke zama al'amudin wuta da dare. Allah yana tare da su kuma yana shiryar da su kowane lokaci sa'anda suke tafiya. Duk abinda za su yi shine su bi shi.
Bayan dan lokaci, Fir'auna da mutanensa suka chanza ra'ayi, sun nemi Isra'ilawa su dawo bauta kuma. Allah ya sa Fir'auna ya taurara zuciyarsa domin dukkan mutane su san cewa shi, Yahweh, shine Allah na gaske, Ikon sa kuma ya sha karfin Fir'auna da allolinsa.
Saboda haka Fir'auna da mayakansa suka bi Isra'ilawa su maishe su bayin su kuma. Da Isra'ilawa sun gan mayakan Masarawa na zuwa, sai suka gane cewa sun fada tarko tsakanin mayakan Msarawa da jan teku. Sai suka tsorata sosai, suka yi kuka, "Me ya sa muka bar Masar? Zamu mutu!"
Musa ya ce wa Isra'ilawa, "Ku bar jin tsoro! Allah zai yi yaki domin ku yau kuma zai cece ku." Sai Allah ya ce wa Musa, "Ka gaya wa Isra'ilawa su yi gaba su nufi jan tekun."
Sai Allah ya matsar da al'amudin girgije ya saka shi tsakanin Isra'ilawa da Masarawa, Masarawa suka kasa ganin Isara'ilawa.
Allah ya ce wa musa ka daga hannunka bisa tekun ka raba ruwayen, sai Allah ya sa iska ta raba tekun zuwa hagu da dama, sai hanya ta kasance a tsakiyan tekun.
Isra'ilawa suka wuce a busassar kasa a tsakiyan tekun da bagon ruwa a kowace gefe.
Allah ya daga al'amudin girgije sama domin Masarawa suka gan Isra'ilawa na tserewa. Sai Masarawa suka yanke shawara su bi su.
Sai suka bi Isra'ilawa akan hanyan da ya ratsa tekun, amma Allah ya sa Masarawa suka tsorata ya kuma sa karusansu sun makalewa. Sai suka yi ihu, "Mu gudu! Allah na yi wa Isra'ilawa yaki!"
Bayan dukkan Isra'ilawa sun ketare zuwa dayan gefen tuken lafiya, Allah ya ce wa Musa sake mika hannun ka. Da ya yi biyayya, sai ruwan tekun ya rufe mayakan Masarawa, ya koma wurinsa kamar da. Dukkan mayakan Masarawa suka nutse.
Sa'anda Isra'ilawa sun gan cewa Masarawa sun mutu, sai suka dogara ga Allah kuma suka gaskanta cewa Musa annabin Allah ne.
Isra'ilawa sun yi murna da farin ciki sosai domin Allah ya cece su daga mutuwa da bauta! Yanzu sun sami yanci su bauta wa Allah. Isra'ilawa suka yi wakoki masu yawa, suna bukin samun sabuwar yancin su, sun yi yabon Allah domin ya cece su daga mayakan Masarawa.
Allah ya umurci Isra'ilawa su yi bukin idin ketarewa a kowace shekara domin tunawa da nasara da ya basu bisa Masarawa da kuma ceton su daga bauta. Sun yi bukin tawurin yanka dan rago marar lahani, da cin gurasa mara yeast.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Fitowa 12:33-15:21
Bayan da Allah ya jagoranci Isra'ilawa suka ratsa Jan Teku, Ya jagorance su cikin daji zuwa dutsen da ake kira Sinai. Wannan shine dutsen da Musa ya gani daji na konewa da wuta. Mutanen kuwa suka gina alfarwa a karkashin dutsen.
Allah ya ce wa Musa da kuma jama'ar Isra'ila, "Idan za kuyi biyayya da ni ku kuma kiyaye alkawarina, za ku zama mallaka ta mai tamani, rundunan firistoci, kuma al'umma mai tsarki."
Bayan kwanaki uku, bayan da mutanen suka shirya kansu da ruhaniyarsu, Allah ya sauko a kan dutsen sina'i da aradu, da walkiya, da hayaki da busar kaho mai kara. Musa ne kadai aka yarda ya haura kan dutsen.
Sa'annan Allah ya basu alkawarin, ya ce, "Ni ne Yahweh, Allahn ku, wanda ya cece ku daga bauta a Masar. Kada ku bauta wa wassu alloli."
"Kada ku kera gumaka kuma kada ku bauta masu, domin Ni, Yahweh, Allah mai kishi ne. Kada ku yi anfani da sunana a rainannun al'amura. Ku tabbata kun kebe ranar asabar da tsarki. Saboda haka, ku yi dukkan ayyukanku a kwanaki shida, domin rana ta bakwai ranar hutu ce agare ku da kuma na tunawa da ni."
"Ka girmama mahaifin ka da mahaifiyar ka. Kada ka yi kisa. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi karya. Kada ka yi sha'awar matar makwabcin ka, gidan sa, ko wani abinda ke mallakarsa."
Sa'annan Allah ya rubuta wadannan dokoki goma akan Alluna guda biyu kuma ya baiwa Musa. Allah kuma ya bada shari'u da dama da kuma ka'idodi da za'a bi. Idan mutane sunyi biyayya da wadannan shari'u, Allah yayi alkawari cewa zai albarkace su ya kuma kare su. Idan suka ki yin biyayya da su kuma Allah zai hukunta su.
Allah ya sake baiwa Isra'ilawa cikakken kwatancin alfarwa da yake so su kera. Ana kiran ta alfarwar saduwa, kuma yana da dakuna biyu, arabe da baban labule. Babban firist ne kadai ke da iznin shiga dakin da ke bayan labulen, domin Allah na kasancewa awurin.
Duk wanda bai yi biyayya da shari'ar Allah ba zai kawo dabba a bagadi dake gaban alfarwa ta saduwa domin hadaya ga Allah. Firist zai yanka dabbar ya kona a kan bagadi. Jinin dabbar da aka yi hadayan zai rufe zunubin mutumin kuma ya tsarkake mutumin a gaban Allah. Allah ya zabi dan'wan Musa, Haruna, da zuriyar Haruna su zama firistocin sa.
Dukkan jama'a suka amince su yi biyayya da Shari'a da Allah ya basu, su bauta wa Allah shi kadai, su kuma kasance mutanensa na musamman. Amma nan bada jimawa ba bayan da suka yi alkawarin yin biyayya ga Allah, sai suka yi mummunar zunubi.
Kwanaki da dama, Musa yana kan dutsen Sina'i yana magana da Allah. Mutanen kuwa suka gaji da jiran dawowarsa. Sai suka kawo ma Haruna zinariya suka roke shi ya kera masu gumaka!
Haruna ya yi gunkin zinariya mai sifar maraki. Mutanen suka fara bautan gumakan suna mika hadayu ga ita! Allah ya husata dasu kwarai domin zunubin su ya kuwa yi shirin hallaka su. Amma Musa yayi addu'a domin su, Allah ya ji addu'ar sa kuma bai hallaka su ba.
Bayanda Musa ya sauko daga dutsen ya ga gunkin, ya husata kwarai har ma ya murguje allunan nan da Allah ya rubuta dokoki goma akai.
Sa'annan Musa ya daka gunkin ya zama gari, ya zuba garin acikin ruwa kuma ya sa mutanen suka sha ruwan. Allah ya aiko da annuba ga mutanen kuma da yawa suka mutu.
Musa ya kera sabon alluna domin dokoki goma maimakon wadanda suka murguje. Sa'annan ya sake haurawa dutsen kuma yayi addu'a Allah ya gafarta wa mutanen. Allah ya saurari Musa ya kuwa gafarta masu. Musa ya sauko daga kan dutsen da sabon alluna dauke da dokoki goma. Sai Allah ya jagoranci isra'ilawa daga dutsen sina'i zuwa yankin kasar alkawari.
Labari a Littafi Mai Tsarki Daga: Fitowa 19-34
Bayanda Allah ya fada wa isra'ilawa dokokin da yake so su yi biyayya da su a matsayin alkawarin sa da su, suka tafi daga dutsen Sina'i. Allah ya fara jagorar su zuwa yankin kasar alkawari, wanda kuma ake kira kan'ana. Al'amudin girgije na tafiye a gabansu zuwa kan'ana su kuma suna biye da shi.
Allah yayi wa Ibrahim, Ishaku, da Yakubu alkawari cewa zai bada kasar alkawari ga zuri'ar su, amma yanzu akwai kungiyoyin mutane da yawa dake zaune a wurin. Ana kiran su kan'aniwa. Kan'aniwa basu bauta ko su yi biyayya da Allah ba. Suna bautar allolin karya kuma suna yin miyagun abubuwa da yawa.
Allah ya cewa Isra'ilawa, "Lalle ne ku kawar da dukkan Kan'aniwa acikin kasar alkawari. Kada ku yi yarjejjeniyar salama da su kuma kada ku aure su. Lelle ne ku hallakar da dukkan gumakunsu gabaki daya. Idan ba ku yi biyayya da ni ba, zaku bauta ma gumakunsu a maimako na."
Sa'anda Isra'ilawa suka iso gabar Kan'ana, Musa ya zabi mutum goma sha biyu, daya daga kowace kabilar Isra'ila. Ya basu umurni su je lekan asirin kasar su kuma gani yadda ta ke. Su kuma dubi yanayin Kan'aniwa su gani ko suna da karfi ko kasassu.
Mutanen nan goma sha biyu suka yi tafiya cikin Kan'ana kwana arba'in sa'an nan suka komo. Suka fada wa jama'ar, "Kasar na da albarka kuma ga yawan anfani!" Amma goma daga cikin masu lekan asirin suka ce, "Birnin na da karfin gaske kuma mutanen katti ne! Idan muka kai masu hari, tabbas zasu fi karfin mu kuma su kashe mu!"
Nan take Kalibu da Joshua, biyu daga cikin masu lekan asirin, suka ce, "Gaskiya ne mutanen Kan'ana dogi ne kuma karfafa, amma tabbas za mu sha karfin su, Allah zai yi yaki amadadin mu!"
Amma mutanen basu saurari Kalibu da Joshua ba. Suka yi fushi da Musa da Haruna suna cewa, "Me yasa kuka kawo mu wannan mummunar wuri? Da ma mun zauna a Masar maimakon a kashe mu cikin yaki kuma a maida matanmu da yayan mu bayi." Mutanen suna so su zabi wani shugaba dabam wanda zai komar da su Masar.
Allah ya husata kwarai har ma ya zo alfarwar saduwa. Allah yace, "Domin kunyi tawaye agare ni, dukkan mutane zasu yi famar yawo a daji. Banda Joshua da Kalibu, kowane daya dake shekara ashirin ko fiye zai mutu acan kuma ba zai taba shiga kasar alkawarin ba."
Da mutanen suka ji haka, suka tuba don sunyi zunubi. Suka dauki kayan yakinsu suka tafi domin su yaki mutanen Kan'ana. Musa kuwa ya gargade su kada su je domin Allah baya tare da su, amma basu saurare shi ba.
Allah bai tafi tare da su zuwa yakin ba, saboda haka aka yi nasara akan su kuma aka kashe da yawa acikin su. Sa'annan Isra'ilawa suka juya wa Kan'ana baya kuma su ka yi faman yawo a daji har shekaru arba'in.
Cikin shekaru arba'in da mutanen Isra'ila suka yi suna yawo a daji, Allah yana yi masu tanadi. Allah ya basu gurasa daga sama, da ake kira "Manna." Ya kuma aiko da yan tsalwa (wanda suke kananan tsuntsaye) a cikin taronsu domin su sami nama su ci. Cikin dukkan lokacin nan, Allah ya kare kayakinsu da takalmansu daga kodewa.
Allah kuwa cikin al'ajibinsa ya basu ruwa daga dutse. Amma duk da haka, mutanen Isra'ila suka yi gunaguni game da Allah da Musa. Duk da haka, adalcin Allah bisa alkawarinsa ga Ibrahim, da Ishaku da Yakubu bai sake ba.
Wani lokaci sa'adda mutanen suka rasa ruwa, Allah ya ce wa Musa, "Yi magana da dutse, ruwa kuwa zai fito daga ita." Amma Musa bai girmama Allah agaban dukkan mutanen ba ta wurin buga dutsen sau biyu da sanda amaimakon magana da ita. Ruwa kuwa ya fito daga dutsen domin kowa ya sha, amma Allah yana fushi da Musa kuma yace, "Bazaka shiga kasar alkawarin ba."
Bayan da Isra'ilawa suka yi ta zagaya acikin daji har shekaru arba'in, dukkan wadanda suka yi tawaye ga Allah sun mutu. Sa'annan Allah ya jagoranci mutanen zuwa iyakar kasar alkawari kuma. Musa kuwa ya tsufa sosai, sai Allah ya zabi Joshua ya taimake shi da shugabantar mutanen. Allah kuwa yayi wa Musa alkawari da cewa wata rana, zai aiko da wani annabi kamar Musa.
Sa'annan Allah ya ce wa Musa ya haura saman dutsen domin ya kalli kasar alkawarin. Musa kuwa ya kalla kasar alkawarin amma Allah bai yarda masa ya shiga ba. Sa'annan Musa ya mutu, Isra'ilawa kuwa suka yi makokinsa har kwana talatin. Joshua kuwa ya zama sabon shugabansu. Joshua shugaba ne nagari domin ya dogara kuma yana biyayya ga Allah.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Fitowa 16-17; Littafin Kidaya 10-14; 20; 27 Maimaitawar Shari'a 34
A karshe lokaci yayi da yayan Isra'ila za su shiga Kan'ana, kasar alkawari. Joshua ya aiki yan lekan asiri guda biyu zuwa kasar Kan'aniyawa a birnin Yeriko da aka kare da garu mai karfi. A wannan birnin a kwai wata karuwa mai suna Rahab wadda ta boye yan lekan asiri sa'annan ta taimake su suka tsere. Ta yi wannan ne domin ta gaskanta Allah. Suka yi alkawarin su tsare Rahab da Iyalin ta sa'anda yan Isra'ila suka zo domin halaka Yeriko.
Da yan Isra'ila suka haye kogin Urdun domin su shiga kasar alkawari. Allah ya gaya wa Joshua, "Bari Firistoci su tafi da farko." Sa'anda firistocin suka fara takawa cikin kogin Urdun, ruwan da ke fitowa ya tsaya domin yayan Isra'ila su haye zuwa gefen rafi akan busasshiyar kasa.
Bayanda mutanen suka haye kogin Urdun, Allah ya gaya wa Joshua yadda zai kai hari wa birnin Yeriko mai ikon kwarai. Mutanen suka yi biyyaya ga Allah. kamar yadda Allah ya gaya masu su yi, Sojoji da firistoci suka taka a kewaye da birnin Yeriko sau daya a rana har ranaku shida.
To a rana ta bakwai, Isra'ilawa suka kewaye birnin Yeriko sau bakwai kuma, sa'anda suke kewaya birnin na karshe, sojoji suka yi ihu sa'annan firistoci suka busa kahonsu.
Sa'annan ganuwan Yeriko ya fadi kasa! Isra'ilawa suka halakar da komai a birnin kamar yadda Allah ya umurce su. Rahab da iyalinta ne kawai basu halaka ba, wanda suka zama daya daga cikin kashin Isra'ilawa. Sa'anda sauran mutane da ke zama a Kan'ana suka ji da cewa Isra'ilawa sun halaka birnin Yeriko, sai suka firgita da cewa yayan Isra'ila za su kai masu hari su ma.
Allah ya riga ya yi wa Isra'ilawa umurni kada su yi wata yarjejeniya da wata kabila na mutanen Kan'ana. Amma daya daga cikin kabilar mutanen Kan'ana, wadda a ke kiransu Gibiniyawa. Suka yi wa Joshua karya ce wa su daga wata kasa ne mai nisa da Kan'ana. Suka ce wa Joshua ya yi yarjejeniya da su. Joshua da Isra'ilawa ba su tambayi Allah game da ko daga ina ne Gibiniyawa suke ba. Sai Joshua ya yi yarjejeniya da su.
Isra'ilawa suka yi fushi sa'anda suka gane da cewa Gibiniyawan sun rude su, amma sun rike yarjejeniya da suka yi da su domin sun yi alkawarin a gaban Allah. Bayan wadansu lokatai, sarakunan wadansu kabilu a Kan'ana, Amoriyawa, sun ji da cewa Gibiniyawa sun yi yarjejeniya da Isra'ilawa, sai suka hada babban taro sojoji suka je suka kai wa Gibiyan hari. Sai Gibiniyawan suka aika wa Joshua sako da cewa ya taimake su.
Sai Joshua ya tara sojojin Isra'ila suka yi tafiya dukan dare domin su same Gibiniyawan. Da sassafe suka ba wa sojojin Amoriyawa mamaki sai suka kai masu hari.
Allah ya yi yaki wa Isra'ila a wannnan rana, ya sa Amoriyawan sun rude sai ya aika manyan kankaran duwatsu wanda ya kashe Amoriyawan da yawa.
Allah ya tsai da rana a wuri daya a sarari saboda Isra'ilawa su sami isasshen lokaci domin su kashe Amoriyawan Gaba daya. A wannnan rana, Allah ya ci wa Isra'ilawa babban nasara.
Bayan da Allah ya yi nasara da wadannan sojojin, wadansu kabilun Kan'aniyawa suka taru da yawa domin su kai wa Isra'ila hari. Joshua da Isra'ilawa suka kai masu hari suka hallaka su.
Bayan wannan yaki, Allah ya ba wa kowace kabilar Isra'ila sashin su a kasan alkawari. Sai Allah ya ba wa Isra'ila salama a dukkan iyakokinsu.
Sa'anda Joshua ya tsufa, ya kira dukan mutanen Isra'ila tare. Sai ya tunashe mutanen da su yi wajibi da biyayya da alkawarin da Allah ya yi da Isra'ila a Sinai. Mutanen suka yi alkawari su yi biyayya da Allah su kuma bi umurninsa.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Joshua 1-24
Bayan mutuwan Joshuwa, Isra'ilawa sun yi wa Allah rashin biyayya da basu kori sauran Kan'aniyawa ko su kiyaye shari'un Allah ba. Isra'ilawa sun shiga bautan allolin Kan'aniyawa sun manta da Yahweh, Allah na gaskiya. Isra'ilawa ba su da sarki, don haka kowa na yin abin da ya ga dama.
Domin rashin biyayyan da Isra'ilawa suka ci gaba da yi wa Allah, Ya hore su ta wurin ba makiyansu su yi nasara akan su. Makiyan nan sun saci abubbuwa da yawa daga Isra'ilawa, sun hallakar da mallakansu, sun kuma kashe su da yawa. Bayan shekaru da yawa na yi wa Allah rashin biyayya da kuma shan tsanani daga makiya, Isra'ilawa sun tuba sun roki Allah Ya kubutar da su.
Sa'annan Allah ya tanada masu mai kubutarwa wanda ya kubutar da su daga hannun makiyan su, ta haka ne ya kawo salama a kasar. Amma kuma mutanen sun manta da Allah sun koma ga bautar gumaku. Saboda haka Allah Ya yarda Midiyanawa, makiyan su na kurkusa su ka sami nasara akansu.
Midiyanawa kuwa suka dauki dukkan amfanin gonar Isra'ilawa na shekaru bakwai. Isra'ilawa kuwa suka tsorata; suka buya a koguna don kada Midiyanawa su same su. Daga karshe kuwa, sun yi kuka ga Allah domin Ya cece su.
Wata rana, wani mutumin Isra'ila mai suna Gidiyon yana bugun hatsi a asirce don kada Midiyanawa su gani su sace. Mala'ikan Yahweh kuwa ya zo wurin Gidiyon ya ce, "Allah na tare da kai, ya kai babban jarumi. Jeka ka ceci Isra'ila daga hannun Midiyanawa."
Mahaifin Gidiyon kuwa na da bagadi da ke na gumaka. Allah kuwa Ya fada wa Gidiyon ya rushe bagadin. Amma don tsoron mutane, Gidiyon ya jira zuwa maraice. Sa'annan ya rushe bagadin, ya rugurguje shi. Ya kuma gina sabuwar bagadi ga Allah kusa da inda bagadin gumakan nan yake a da, anan ya mika hadaya ga Allah akan ta.
Kashegari mutane sun gano cewa wani ya yaga ya kuma rushe bagadin, sai sun husata. Sun nufa gidan su Gidiyon domin su kashe shi, amma mahaifin Gidiyon yace, "Me ya sa kuna kokarin ku taimaki allahnku? Indai shi allah ne, ya kare kansa mana!" Fadinsa haka, mutanen basu kashe Gidiyon kuma ba.
Midiyanawa kuwa suka kuma zuwa don yin sata daga Isra'ilawa. Yawansu ya fi gaban a kirga. Gidiyon kuwa yayi kira ga Isra'ilawa su yake su. Gidiyon ya nemi alamu biyu daga wurin Allah don samun tabbacin Allah zai more shi don ya ceci Isra'ila.
Alama ta farko, Gidiyon ya shimfida fatar tunkiya a kasa, ya roki Allah Ya bar rabar safiya ya sauka akan fatan tunkiyar kadai ban da a kasa. Allah yayi haka. Dare na biye, yayi roko yana so kasa ne kawai da raba, fatan tunkiya kuma a bushe. Allah Ya sake yin haka. Wadannan alamu biyu sun tabbatar wa Gidiyon da cewa Allah zai yi amfani da shi don ceton Isra'ila daga Midiyanawa.
Sojojin Isra'ila 32,000 suka zo wurin Gidiyon, amma Allah Ya gaya masa cewa sun yi yawa. Saboda haka Gidiyon ya komar da 22,000 gida da ke tsoron yaki. Allah Ya kuma ce wa Gidiyon, har yanzu mutanen na da yawa. Saboda haka Gidiyon ya komar da dukkan su gida, sai sojoji 300 ne kawai ya bari.
A wannan dare kuwa, Allah Ya gaya wa Gidiyon, "Jeka sansanin Midiyanawa, in ka ji abin da suka ce, ba zaka ji tsoro kuma ba." A cikin daren, Gidiyon ya nufi sansanin, ya ji wani sojan Midiyanawa na fada wa abokin sa mafarkin da yayi. Abokin mutumin ya ce, "Ma'anar wannan mafarkin shi ne, mayakan Gidiyon zasu ci mayakan Midiyanawa da yaki!" Da Gidiyon ya ji haka, yayi sujada ga Allah.
Da Gidiyon ya komo wurin sojojin sa, ya ba kowannen su kaho, tukunyar kasa, da kuma tocila. Sun kewaye sansani inda sojojin Midiyanawa na sharan barci. Sojojin Gidiyon 300 suna da tociloli cikin tukwane, a yadda Midiyanawa ba za su iya ganin hasken tocilolin ba.
Sa'annan, sojojin Gidiyon duka suka farfashe tukwanen su a lokaci daya, nan da nan kuma wutan tocilolin ya bayyana. Suka busa kaho suka yi ihu suna cewa, "Takobin Yahweh da na Gidiyon!"
Allah Ya kawo rudani ga Midiyanawa, sun fara kai wa juna hari suna kashe junan su. Nan da nan, an kirawo sauran Isra'ilawa daga gidajen su domin su taimaka wurin koran Midiyanawa. Sun kashe masu yawan su, sun kuma kori sauran, sun fitar da su daga kasar Isra'ilawa. Midiyanawa 120,000 ne suka mutu a ranar. Allah ya ceci Isra'ila.
Mutanen na so su nada Gidiyon sarkin su. Gidiyon bai yarda masu ba, amma ya roki zobba na zinariya da kowannen su ya dauka daga wurin Midiyanawa. Mutanen sun ba Gidiyon zinariya masu yawan gaske.
Gidiyon kuwa yayi amfani da zinariyar wurin yin tufafi na musamman, irin da babban firist ke sa. Amma mutane sun fara wa tuffan sujada kamar ga gumaka. Saboda haka Allah Ya hori Isra'ila kuma, domin suna bauta wa gumaku. Allah Ya bar makiyan su su sami nasara akansu. A karshe su ka roki Allah Ya taimake su, Allah kuma Ya aika masu wani mai kubutarwa.
Wannan yanayi ya maimaita kansa sau da dama: Isra'ilawa za su yi zunubi, Allah kuma Ya hore su, za su tuba, Allah kuma Ya aika mai kubutarwa ya cece su. Shekaru da dama Allah na aikan masu kubutarwa da ke ceton Isra'ilawa daga makiyan su.
A karshe, mutanen sun roki Allah Ya ba su sarki kamar yadda sauran al'ummai ke da shi. Suna neman sarki wanda ke da tsayi da kuma karfi, wanda kuma zai jagorance su zuwa yaki. Allah bai ji dadin wannan rokon na su ba, amma Ya ba su sarki irin da suke so.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Mahukunta 1-3; 6-8
Saul shi ne sarki na farko a Isar'ila. mai tsayi ne shi, kyakkyawa ne kamar yarda mutane ke so. Saul sarki ne na gari a farkon shekaru a mulkinsa bisa Isar'ila. Amma ya zama mugu mutum wanda ba ya biyayya da Allah, Allah ya zabi wani mutum dabam wanda wata rana zai zama sarki amadadinsa.
Allah ya zabi wani matashin Isar'ila, mai suna Dauda ya zama sarki bayan Saul. Dauda makiyayi ne daga garin Baitalami . A lokaci dabam dabam yayin da yake kiwon tumakin mahaifinsa, Dauda ya kashe zaki da biyer da su ka kai hari ga tumakin. Dauda mutum ne mai tawali'u da adalci wanda ya dogara yana kuma biyayya da Allah.
Dauda ya zama jarumin soja da kuma shugaba. Sa'anda Dauda ke matashi, ya yi fada da katon nan mai suna Goliya. Goliya hurarren soja ne, kakkarfa tsayinsa misali kamu uku! Amma Allah ya taimake Dauda ya kashe Goliya, ya kuma ceci Isar'ila. Bayan wancen, Dauda ya yi nasarori da yawa akan abokan gaban Isar'ila, don wannan mutane ke yabon sa.
Saul yana kishi da kaunar da mutane ke yi wa Dauda. sau da yawa Saul ya yi kokarin kashe shi, sai Dauda ya boye wa Saul . Wata rana, Saul na neman Dauda domin ya kashe shi. Saul ya je kogon da Dauda ke boye wa daga Saul, Amma Saul bai gan shi ba. Amma Dauda na nan kusa da inda Saul ya ke, zai iya kashe shi, amma bai yi ba. Maimakon haka, Dauda ya dauke yankin rigar Saul ya tabbatar ma sa cewa ba zai kashe shi don ya zama sarki ba.
Bayan mutuwar Saul a yaki, sai Dauda ya zama sarkin Isar'ila. Shi sarki ne na gari, kuma mutane na kaunarsa. Allah ya albarkace Dauda, ya kuma bunkasa. Dauda ya yi yake yake da dama, Allah ya kuma taimake shi ya ci nasara akan abokan gaba na Isar'ila. Dauda ya ci nasara abisa Urushalima ya mishe shi babban barin kasarsa. Alokacin da Dauda ke mulkin, Isar'ila sun zama masu iko da arziki.
Dauda ya so ya gina haikali inda dukan Isar'ilawa za su bauta wa Allah, su kuma mika masa hadayu. Kimanin shekaru dari hudu (400), mutane sukan bautawa Allah, da kuma mika masa hadayu a alfarwa ta saduwa wanda Musa ya gina.
Amma Allah ya aika anabi Nathan zuwa ga Dauda da wannan sako, "Saboda kai dan yaki ne, ba za ka iya gina mani wannan haikalin ba. Danka ne zai gina shi. Amma, zan albarkace ka kwarai. Daya daga zuri'ar zai yi mulki amatsayin sarki bisa mutane na har abada!" Almasihu ne kadai ke da ikon mulki na har abada a zuri'ar Dauda. Almasihu zabbabe dan Allah wanda zai ceci mutanen duniya daga zunubinsu.
Sa'anda Dauda ya ji wadannan kalmomi, Nan da nan ya yi godiya, da yabo ga Allah domin ya yi wa Dauda wannan alkawari mai girma da daraja da albarku masu yawa. Dauda bai san lokacin da Allah zai yi wadannan abubuwa ba. Amma yadda ya kasance, sai Isar'ilawa za su yi jira na tsawon lokaci kafin zuwan Almasihu, kusan shekaru dubu daya (1,000).
Dauda ya yi mulkinsa da adalci da kuma aminci na shekaru da dama, kuma Allah ya albarkace shi. Duk da haka, a karshen rayuwarsa ya yi mummunar zunubi ga Allah.
Wata rana, sa'anda dukan sojojin Dauda sun tafi yaki nisa da gida, ya duba daga cikin fadarsa, sai ya ga wata kyakkyawar mace tana wanka. Mai suna Batsheba.
A maimakon kau da hankalin sa, Dauda ya aika da wani ya kawo ta a gare shi, ya kwana da ta, sai ya sallame ta kuma ta koma agida. Bayan lokaci kadan Batsheba ta aika da sako zuwa ga Dauda cewa tana da juna biyu.
Mai gidan Batsheda, mutum ne mai suna Uriya, yana cikin daya daga kwararon sojojin Dauda. Dauda ya kira Uriya ya dawo daga yaki, sai ya gaya masa ya je ya kasance da matarsa. Amma Uriya ya ki ya je gida, yayin da sauran sojoji na yaki. Sai Dauda ya tura Uriya gurin yaki ya gaya wa shugaban sojojin ya sa shi inda abokan gaba ke da karfi don a kashe shi.
Bayan an kashe Uriya, Dauda ya auri Batsheba.Ta haifa wa Dauda da. Allah ya yi fushi da Dauda a game da abin da ya yi, sai ya aiki Annabi Nathan ya gaya wa Dauda irin mugun zunubi da ya yi. Dauda ya tuba daga zunubinsa kuma Allah ya gafarce shi. Dukkan rayuwar sa, Dauda ya yi tafiya, kuma ya yi biyayya ga Allah, har ma a lokacin tsanani.
Amma, a game da hukuncin zunubin Dauda, dan da ya haifa, ya mutu. Fada tsakanin iyalin Dauda har karshen rayuwar sa, ikon Dauda ya zama mara karfi. Ko da shike Dauda mara aminci ne ga Allah, Allah mai amince ne ga alkawaransa. Daga baya, Dauda da Batsheba son sami wani yaro, su ka sa masa suna Sulaimanu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: 1Samaila 10; 15-19; 24; 31; 2 Samaila 5; 7; 11-12
Bayan shekaru masu yawa, Dauda ya mutu, sai yaron sa Sulaimanu ya fara mulki bisa Isra'ila. Allah ya yi magana da Sulaimanu ya tambaye shi abinda ya fi so. Sa'anda Sulaimanu ya bida hikima, Allah ya ji dadi sai ya mayar da shi mafi hikima a dukan duniya. Sulaimanu ya koyi abubuwa masu dama ya kuma zama alkali mai hikima kwarai. Allah kuma ya azurta shi sosai.
A Urshelima, Sulaimanu ya gina haikali da mahaifinsa Dauda ya shirya ya kuma tara kayaki. Yanzu mutane suna wa Allah sujada suna kuma mika masa hadaya a haikalin a maimakon yinsa a alfarwar saduwa. Allah ya sauko ya kasance a haikalin, ya kuma zauna a can da mutanensa.
Amma Sulaimanu ya kaunaci mata daga wassu kasashe. Ya yi rashin biyayya ga Allah ta wurin aurayar mata da yawa, kimanin 1,000! da yawa daga cikin matan sun zo ne daga kasashen wuje kuma suka kawo allolinsu tare da su suka kuma cigaba da bauta masu. Sa'anda Sulaimanu ya tsufa, shi ma ya bauta wa allolinsu.
Allah ya yi fushi da Sulaimanu, domin horon Sulaimanu don rashin amincinsa, ya yi alkawari zai raba kasar Isra'ila kashi biyu bayan mutuwar Sulaimanu.
Bayanda Sulaimanu ya mutu, yaronsa, Rerobowam, ya zama sarki. Rerobowam mutum ne mai wauta. Dukan mutanen kasar Isra'ila sun hada kai domin su tabatar da zamansa sarki. Sun kai kukansu ga Rerobowam cewa Sulaimanu ya sa su aiki mai wahala suna kuwa biyan haraji mai yawa.
Rerobowam ya yi wautar basu amsa, "Ku na tsamani mahaifina Sulaimanu ya nawauta maku da aiki mai wahala, amma ni zan nawauta maku da aiki mafi wuya da na shi, kuma zan ba ku azaba sosai fiye da shi."
Kabila guda goma na kasar Isra'ila suka tayar wa Rerobowam. Kabila biyu ne suka kasance masu aminci gareshi shi. Wadannan kabilu biyun suka kasance mulkin Yahuza.
Sauran kabilu goman na kasar Isra'ila da suka tayar wa Rerobowam suka zabe wani mutum mai suna Jerobowam ya zama sarkinsu. suka sa mulkin a gefen arewacin kasar kuma suka kira shi mulkin Isra'ila.
Jerobowam ya tayar wa Allah ya kuma sa mutane sun yi zunubi. Ya gina gumaka biyu domin mutane su bauta masu maimakon su bauta wa Allah a haikali a mulkin Yahuza.
Mulkin Yahuza da na Isra'ila suka zama abokan gaba sukan yi yaki da juna.
A sabon mulkin Isra'ila, duka sarakunan mugaye ne. Da yawa daga cikin wadannan sarakunan yan Isra'ila ne suka kashe su wadanda su ke so su zama sarki a maimakon su.
Duka sarakuna da yawanci mutanen da ke mulkin Isra'ila sun bauta wa gumaka. Bautar gumakarsu ya s suna zina har wassu lokatai suna hadaya da yaya.
Sarakunan Yahuza daga zuriyar Dauda su ke, wadansu sarakunan mutane ne masu hankali wadanda suka yi mulki ciki adalci suka kuma bauta wa Allah. Amma yawancin sarakunan Yahuza mugaye ne kuma masu rashawa, sun bauta wa gumaku. Wadansu sarakunan sun yi hadaya da yaran su wa allolin karya. Yawanci mutanen Yahuza sun tayar wa Allah suka bauta wa wassu alloli.
Labari a Littafi Mai Tsaki daga: 1 Sarakuna 1-6; 11-12
A duk tarihin Isra'ilawa,' Allah ya aika masu annabawa. Annabawan sukan ji sakonni da ga Allah sai fada wa mutane sakonnin Allah.
Iliya annabi ne lokacin da Ahab yake sarki bisa mulkin Isra'ila. Ahab mugun mutum ne wanda ya iza mutane su bauta wa allahn karya, da ake kira Ba'al. Iliya ya ce wa Ahab, "Ba za a yi ruwa ko raba a mulkin Isra'ila ba sai a fada ta." Wannan ya sa Ahab ya yi fushi kwarai.
Allah ya ce wa Iliya ya tafi wani rafi cikin jeji ya boye daga Ahab wanda yake so ya kashe shi. Kowacce safiya da kowacce yammaci, tsuntsaye za su kawo masa gurasa da nama. Ahab da sojojinsa suka nemi Iliya amma basu iya samunsa ba. Farin ya yi tsanani har a karshe rafin ya bushe.
Sai Iliya ya tafi wata makwabciyar kasa. Wata gwauruwa da danta a kasar abincinsu ya kusa karewa saboda rashin ruwan sama ya kawo fari. Amma suka lura da Iliya, Allah kuma ya tanada masu, har garin tukunyarsu da man kwalbarsu basu kare ba. Sun kasance da abinci dukkan kwanakin farin. Iliya ya zauna can shekaru da dama.
Bayan shekaru uku da rabi, Allah ya gaya wa Iliya ya koma kasar Isra'ila ya yi magana da Ahab domin zai aiko da ruwan sama kuma. Da Ahab ya ga Iliya ya ce, "Gaka nan, mai tada hankali!" Iliya ya amsa masa ya ce, "Kai ne mai tada hankali! Ka yashe da Yaweh Allahn gaske, ka yi wa Ba'al sujada. Kawo dukkan mutanen kasar Isra'ila zuwa Dutsen Karmel"
Dukkan mutanen kasar Isra'ila, har ma da annabawan Ba'al 450, suka zo Dutsen Karmel. Iliya ya ce wa mutanen, "Har yaushe zaku dinga sauya ra'ainku? Idan Yaweh shine Allah, ku bauta masa! Idan Ba'al Allah ne ku bauta masa!"
Sai Iliya ya ce wa annabawan Ba'al, "Ku yanka sa, ku shirya shi domin hadaya, amma kada ku hura wuta. Nima zan yi haka. Allahn da ya amsa da wuta shine Allah na gaske." Sai firistocin Ba'al suka shirya hadaya, amma basu hura wuta ba.
Sai annabawan Ba'al suka yi addu'a ga Ba'al, "Ka ji mu Ba'al!" Dukkan yini suka yi ta addu'a da kuma ihu, har ma suka yi ta yayanka kansu da wukake, amma babu amsa.
A karshen ranar, Iliya ya shirya hadaya ga Allah. Sai ya ce wa mutanen su zuba ruwa manyan randuna goma sha biyu bisa hadayar har sai naman, da itacen, da kuma kasar dake kewaye da bagaden sun jike gaba daya.
Sai Iliya ya yi addu'a, "Yahweh, Allah na Ibrahim, da Ishaku,da Yakubu, ka nuna mana yau cewa kai ne Allah na Isra'ila, ni kuma bawanka ne. Ka amsa mini domin wadannan mutane, su sani kai ne Allah na gaske."
Nan take wuta ta fado daga sama, ta kone naman da itacen da duwatsun da kurar har ma da ruwan da ke kewaye da bagaden. Da mutanen suka ga haka, suka fadi a kasa, suka ce, "Yahweh shine Allah! Yahweh shine Allah!"
Sai Iliya ya ce, "Kada ku bar ko wani daga annabawan Ba'al ya kubce!" Sai mutanen suka kama annabawan Ba'al suka dauke su daga wurin suka kashe.
Sai Iliya ya ce wa Sarki Ahab, "Koma maza cikin birni domin ruwan sama na zuwa." Bada jimawa ba sai sama ta yi baki aka soma ruwan sama mai karfi. Yahweh ya tsaida fari ya tabbatar da cewa shine Allahn gaske.
Bayan zamanin Iliya, Allah ya zabi wani mutum mai suna Elisha ya zama annabinsa. Allah ya yi al'ajibai masu yawa ta wurin Elisha. Daya daga cikin al'ajiban ya faru ne da Na'aman, shugaban magabta, wanda yake da mummunar ciwon fata. Ya ji labarin Elisha, sai ya tafi ya roki Elisha ya warkar da shi. Elisha ya gaya wa Na'aman ya tsoma kansa sau bakwai a kogin Urdun.
Da fari Na'aman ya yi fushi, ya so ya ki domin ya ga kamar wauta ce. Daga baya ya sauya ra'ayinsa ya tsunduma kansa sau bakwai a kogin Urdun. Da ya fito ana karshe fatarsa gaba daya ta warke! Allah ya warkar da shi.
Allah ya aiki wassu annabawa da yawa. Dukkansu suka gaya wa mutanen su daina bautar gumaku, su fara nuna adalci da jinkai ga wassu. Annabawan sun yi wa mutanen gargadi cewa idan basu bar yin mugunta ba, su soma biyayya da Allah, Allah zai shari'antasu, masu laifi, ya kuma hukuntasu.
Yawancin lokaci mutanen basu yi biyayya da Allah ba. Sau da yawa sukan wulakanta annabawan a wassu lokatan kuma har su kashe su. A wani lokaci an taba sa annabi Irimiya a wata busasshiyar rijiya, aka bar shi ya mutu a wurin. Ya nutse a cikin laka dake kasan rijiyar, amma dai sai sarki ya yi masa jinkai, ya umarci barorinsa su ciro Irimiya daga rijiyar kafin ya mutu.
Annabawan suka cigaba da magana domin Allah, koda shike mutane sun ki su. Suka fadakar da mutane cewa Allah zai hallakar da su idan ba su tuba ba. Suka kuma tunatar da mutane game da alkawarin cewa Almasihu na Allah zai zo.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: 1 Sarakuna 16-18; 2 Sarakuna 5; Irimiya 38
Mulkin Isra'ila da mulkin Yahuza duka biyu suka yi wa Allah zunubi. Suka karya wa'adin da Allah ya riga ya yi da su a Sina'i. Allah ya aiki annabawansa suyi masu gargadi su tuba, su yi masa sujada kuma, amma suka ki yin biyayya.
Saboda haka Allah ya hori mulkokin biyu ta wurin barin magabtansu su hallakasu. Sarautar Assuriyawa, masu karfi, muguwar kabila, suka hallakar mulkin Isra'ila. Assuriyawa suka kashe mutane da yawa cikin mulkin Isra'ila, suka kwashe dukan abubuwa masu tamani, suka kuma kona yawancin kasar.
Assuriyawa suka tara dukan shugabanni, da mawadata da masu fasaha suka kai su Assuriya. Talakawa ainun kadai na Isra'ilawa da ba a kashe ba aka bari a kasar Isra'ila.
Sai Assuriyawa suka kawo bare su zauna a kasar inda mulkin Isra'ila da ya kasance. Baren suka sake gina rusasssun biranen suka auri Isra'ilawan da aka bari a wurin. Aka kira zuriyar Isra'ilawa da suka auri bare, Samariyawa.
Mutane dake yankin mulkin Yahuza sun ga yadda Allah ya hukunta mutanen da ke mulkin Isra'ila saboda basu gaskanta shi ba kuma basu yi masa biyayya ba suka cigaba da bautar gumaku, har da allolin Kan'aniyawa. Allah ya aiki annanabawa su gargade su, amma suka ki ji.
Kimanin shekaru 100 bayan da Assuriyawa suka hallakar da mulkin Isra'ila, Allah ya aika Nebukanezar Sarkin Babila ya kawo hari wa mulkin Yahuza. Babila mulki ce mai karfi. Sarkin Yahuza ya yarda ya zama bawan sarki Nebukanezar, ya kuma biya shi kudi mai yawa kowace shekara.
Amma bayan 'yan shekaru, sarkin Yahuza ya yi tawaye wa Babila. Sabo da haka mutanen Babila suka dawo suka kai wa mulkin Yahuza hari. Suka ci birnin Urushalima da yaki, suka rushe Haikalinsu, suka kwashe duk arzikin garin da na Haikalin.
Domin a hukunta sarkin Yahuza saboda ya yi tawaye, sojojin Nebukanezar suka kashe 'yayan sarki maza a gabansa, sa'annan suka makantar da shi. Bayan haka suka tafi da sarki zuwa Babila ya mutu a kurkuku.
Nebukanezar da sojojinsa suka kwashe kusan dukan mutane mulkin Yahuza zuwa Babila, suka bar mutane mafi talauci kadai a baya domin su noma kasar. Wannan lokaci da aka tilasta wa mutanen Allah su bar Kasar Alkawari, ana kiransa, "Bautar Talala"
Ko da shike Allah ya hukunta mutanensa domin zunubansu, ta wurin kai su bautar talala, bai manta da su ba ko kuma alkawaransa. Allah ya ci gaba da lura da mutanensa yana masu magana ta wurin annabawansa. Ya yi alkawarin cewa bayan shekaru saba'in, za su sake komawa Kasar Alkawari.
Da misalin shekaru saba'in suka wuce, Sairus, Sarkin Fasha, ya yi nasara da Babila, sai sarautar Fasha ta maye gurbin sarautar Babila. A lokacin ne aka kira Isra'ilawa Yahudawa kuma yawancinsu sun yi dukkan rayuwarsu a Babila. Sai dai kima daga cikin Yahudawan da suka tsufa sosai, suka ma tuna da kasar Yahuza.
Sarautar Fasha tana da karfi, amma ta na da jinkai ga wadanda ta mallaka. Bayan dan lokaci kadan da Sairas ya zama sarkin Fasha, sai ya bada umarni cewa duk Bayahuden da ke so ya koma Yahuza zai iya barin Fasha ya koma Yahuza. Har ma ya basu kudi su sake gina Haikali! Saboda haka bayan shekaru 70 na bautar talala, karamin kungiyar Yahudawa suka dawo birnin Urushalima a Yahuza.
Da mutanen, suka iso cikin Urushalima, suka sake gina Haikali da ganuwa kewaye da birnin. Koda shike har yanzu suna karkashin mulkin wadansu mutane, amma dai sun sake zama a cikin Kasar Alkawari, suna sujada a Haikali.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: 2 Sarakuna 17:24-25; 2 Tarihi 36; Ezra 1-10; Nehemiya 1-13
Tun daga farko, Allah ya yi shirin aiko da Almasihu. Alkawarin farko na Almasihu ya zo ga Adamu da Hauwa'u. Allah yayi alkawari cewa za'a haifi zuri'ar Hawa'u wanda zai kuje kan macijin. Macijin da ya yaudari Hauwa'u Shaidan ne. Ma'anar alkawarin shine Almasihu zai yi nasara akan Shaidan gaba daya.
Allah yayi wa Ibrahim Alkawari cewa ta wurin sa duk kabilun mutanen duniya zasu sami albarka. Wannan Alkawari zai cika yayinda Almasihu zai zo nan gaba. Zai ba wa mutane na dukkan kabilun duniya damar su sami ceto.
Allah ya yi wa Musa alkawari cewa nan gaba zai tada wani annabi kamar Musa. Wannan wani alkawari ne kuma game da Almasihu wanda zai zo wani lokaci nan gaba.
Allah yayi wa Sarki Dauda alkawari cewa daya daga cikin zuriyarsa zai yi mulki kamar sarki a bisa mutanen Allah har abada. Wannan ya nuna cewa Almasihun zai zama daya daga cikin zuriyar Dauda.
Ta wurin annabi Irimiya, Allah yayi alkawari cewa zai yi sabon Wa'adi, amma ba kamar Wa'adin da yayi da Isra'ila a Sina'i ba. A wannan Sabon Wa'adi, Allah zai rubuta shari'arsa a zukatan mutane, mutanen kuma zasu san Allah da kansu, zasu zama jama'arsa, Allah kuma zai gafarta masu zunuban su. Almasihu ne zai fara Sabon Wa'adi.
Annabawan Allah kuma sun ce Almasihun zai zama annabi, firist, da kuma sarki. Annabi mutum ne da ke jin kalmomin Allah sa'annan ya sanar da kalmomin Allah ga mutane. Almasihu wanda Allah yayi alkawari zai aiko zai zama cikakken annabi.
Firistocin Isra'ila sun mika hadayu ga Allah a madadin mutane a maimakon hukuncin zunubansu. Firistoci kuma sun yi addu'a ga Allah domin mutane. Almasihu zai zama cikakken babban firist wanda zai mika kansa cikakken hadaya ga Allah.
Sarki mutum ne mai sarauta akan mulki yana kuma shar'ianta mutane. Almasihu zai zama cikakken sarki da zai zauna akan kursiyin kakan kakaninsa Dauda. Zai yi mulki bisa duniya duka har abada, kuma a koyaushe zai yi shari'ar gaskiya ya kuma yanke shawara da adalci.
Annabawan Allah sun yi anabcin wassu abubuwa da yawa game da Almasihu. Annabi Malakai yayi anabcin cewa wani babban annabi zai zo kafin zuwan Almasihu. Annabi Ishaya yayi anabci cewa za'a haifi Almasihu ta wurin budurwa. Annabi Mika yace za'a haife shi cikin birnin Baitalami.
Annabi Ishaya ya ce Almasihu zai zauna a Galili, ya ta'azantar da mutane masu karyayyar zuciya, yayi shelar yanci ga daurarru da kuma saki ga wadanda ke kurkuku. Ya kuma yi annabci cewa Almasihun zai warkar da mutane masu ciwo da wadanda ba sa iya ji, gani, magana, ko tafiya.
Annabi Ishaya kuma yayi annabci cewa za'a tsani Almasihu ba dalili a kuma ki shi. Wadansu annabawa sun yi annabci cewa wadanda zasu kashe Almasihu zasu yi kuri'a akan tufafinsa sa'annnan kuma wani amini zai ci amanarsa. Annabi Zakariya yayi annabci cewa za'a biya aminin tsabar azurfa talatin a matsayin hakin cin amanar Almasihu.
Annabawan kuma sun fadi yadda Almasihu zai mutu. Ishaya yayi annabci cewa mutune zasu tofa masa yawu, suyi masa ba'a, su kuma doddoki Almasihun. Za su soke shi zai kuma mutu cikin azaba mai tsanani da radaddi, ko da shike bai yi wani laifi ba.
Annabawan kuma sun ce Almasihun zai zama cikakke, marar zunubi. Zai mutu domin ya dauki hukunci na zunuban wassu mutane. Hukuncinsa zai kawo salama tsakanin Allah da mutane.Saboda wanan dalili, nufin Allah ne ya kuje Almasihu.
Annabawan sun yi annabci cewa Almasihun zai mutu, Allah Kuma zai tashe shi daga matattu. Ta wurin mutuwar Almasihu da tashinsa, Allah zai kammala shirinsa na ceton masu zunubi, ya kuma fara Sabon Wa'adin.
Allah ya bayyana wa annabawa abubuwa da yawa game da Almasihu, amma Almasihu bai zo a lokacin da ko daya daga cikin annabawan nan na nan ba. Fiye da shekaru 400 bayan an bada annabci na karshe, a cikar lokaci daidai, Allah zai aiko da Almasihu cikin duniya.
Labari a Littafi Mai Tsarki Daga: Farawa 3:15; 12:1-3; Maimaitawar Shari'a 18:15; 2 Sama'ila 7; Irimiya 31; Ishaya 59:16; Daniyel 7; Malakai 4: 5; Ishaya 7:14; Mika 5: 2; Ishaya 9:1-7; 35:3-5; 61;53; Zabura 22:18; 35:19; 69:4; 41:9; Zakariya 11:12-13; Ishaya 50:6; Zabura 16:10-11
A zamanin da, Allah yayi magana da mutanensa ta wurin mala'iku da annabawa. Amma shekaru 400 suka wuce da bai yi masu magana ba. Ba labari sai wani mala'ika ya zo da sako daga Allah zuwa warin tsohon firist mai suna Zakariya. Zakariya da matarsa, Alisabatu, mutane masu tsoron Allah ne, amma ba ta iya ta sami yara ba.
Sai mala'kan yace wa Zakariya, "Matar ka zata sami yaro. Za ka sa masa suna Yahaya. Za'a cika shi da Ruhu Mai Tsarki, kuma zai shirya mutane domin Almasihu!" Zakariya ya amsa, "Matata da ni mun tsufa ainun har da zamu sami yara! Yaya zan san wannan zai faru?"
Sai mala'ikan ya amsa wa Zakariya, "Allah ne ya aiko ni, in kawo maka wannan labari mai dadi. Saboda ba ka gaskanta da ni ba, ba zaka iya yin magana ba har sai an haifi yaron. "Nandanan Zakariya ya kasa yin magana. Sai mala'ikan ya bar Zakariya. Bayan wannan, Zakariya ya koma gida matarsa kuma ta sami ciki.
Sa'anda Alisabatu tana da ciki wata shida, wannan Mala'ikan ba zato ya sake bayyana ga `yar'uwar Alisabatu wanda sunanta Maryamu. Ita budurwa ce wadda ke da alkwarin aure da wani nutum mai suna Yusufu. Sai mala'ikan ya ce, "Za ki yi ciki kuma ki haifi 'da. Za ki ba shi suna Yesu. Zai zama 'Dan Madaukaki Allah zai kuma yi mulki har abada."
Maryamu ta amsa, "Yaya wannan zai kasance da shike ni budurwa ce?" Mala'ikan yayi bayyani, "Ruhu Mai Tsarki zai zo gare ki, ikon Allah kuma zai lullube ki. Ta haka jaririn zai zama mai tsarki, 'Dan Allah." Maryamu ta gaskanta ta kuma amince da abinda Mala'kan ya fada.
Ba da jimawa ba bayan mala'ikan yayi magana da Maryamu, sai ta tafi ta ziyarci Alisabatu. Da jin muryar gaisuwar Maryamu, sai jaririn Alisabatu yayi tsalle a cikinta. Matan suka yi murna tare game da abinda Allah ya riga yayi dominsu. Bayan wata uku da Maryamu ta ziyarci Alisabatu, Maryamu ta koma gida.
Bayan Alisabatu ta haifi danta namaiji, Zakariya da Alisabatu suka ba jaririn suna Yahaya, kamar yadda mala'ika ya umarta. Sai Allah ya yarda wa Zakariya yayi magana kuma. Zakariya yace, "Yabo ga Allah, domin ya tuna da mutanensa! Kai, da na, za a kira ka annabin Madaukaki Allah wanda zai gaya wa mutane yadda zasu karbi gafara domin zunubansu!''
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Luka 1
Maryamu tana da alkawarin aure da wani adali mai suna Yusufu. Sa'anda ya ji cewa Maryamu tana da juna biyu, ya sani cewa jaririn dake cikin ta ba na sa bane. Baya so ya kunyatar da Maryamu, sai ya yi shirin ya saketa a asirce. Kafin ya yi haka, Mala'ika ya zo ya yi magana da shi a mafarki.
Mala'ikan yace, "Yusufu, kada ka ji tsoron daukar Maryamu, a matsayin matar ka. Jaririn dake cikinta daga Ruhu Mai Tsarki ne. Zata haifi 'da. Ka sa masa suna Yesu (ma'ana, 'Yahweh mai ceto'), domin zaya ceci mutane daga zunuban su."
Sai Yusufu ya auri Maryamu ya kuma kawo ta gida a matsayin matarsa, amma bai santa ba, har sai da ta haihu.
Sa'adda Maryamu ta kusa haihuwa, sai masu mulkin Roma suka umurci kowa ya je kidaya a birnin da kakanninsu suka zauna. Yusufu da Maryamu suka yi tafiya mai nisa daga inda suke zama a Nazaret, zuwa Baitalami domin Dauda ne kakan su, kuma Baitalami ne garin su.
Da suka isa Baitalami, ba su sami masauki ba. Dakin da suka samu kawai shine mazaunin dabbobi. Aka haifi jaririn a wurin, mahaifiyar kuma ta shimfida shi a kwami, da shike basu da gado domin shi. Suka sa masa suna Yesu.
Cikin daren nan, akwai wadansu makiyaya a fage kusa da su suna tsaron dabbobin su. Nan da nan, wani mala'ika mai walkiya ya bayyana a gare su, sai suka firgita. Sai mala'ikan ya ce, "Kada ku ji tsoro, domin ina da labari mai dadi domin ku. An haife Almasihu, Ubangiji, a Baitalami!"
''Ku je ku nemi jaririn, za ku kuma same shi a nannade cikin tsummokara yana kwance a kwami." Nan da nan, sararin sama ta cika da mala'iku suna girmama Allah, suna cewa, "Daukaka ta tabbbata ga Allah a sama, da salama a duniya, ga mutanen da ya yi wa tagomashi!"
Nan da nan makiyayan kuwa suka iso wurin da Yesu yake, sai suka same shi a kwance cikin kwami, kamar yadda mala'ikan ya fada masu. Su ka cika da murna. Makiyayan suka koma fagen da tumakansu suke, su na yabon Allah domin dukkan abubuwan da suka ji suka kuma gani.
Bayan wani lokaci, masana daga kasashe masu nisa a gabas, suka ga wani bakon tauraro a sararin sama. Suka gane cewa ma'anar haka itace an haifi sabon sarkin Yahudawa. Sai suka yi tafiya mai nisa domin su ga wannan sarkin. Suka zo Baitalami suka sami gidan da Yesu da iyayensa suke zama.
Sa'anda masanan suka ga Yesu da mahaifiyar sa, sai suka rusuna suka yi masa sujada. Suka ba wa Yesu kyautai masu tsada. Sa'annan suka koma gida.
Labari a Litafi Mai Tsarki daga: Matta 1; Luka 2
Yahaya, 'dan Zakariya da Alisabatu, ya yi girma ya kuma zama annabi. Yayi rayuwa cikin jeji, yana cin zuma da fara, ya na kuma sanye da tufafin da aka yi da gashin rakumi.
Mutane da dama suka fito zuwa jejin domin su saurari Yahaya. Sai ya yi masu wa'azi, ya na cewa, "Ku tuba domin mulkin Allah ya kusa!"
Da mutane suka ji sakon Yahana, da yawa daga cikinsu suka tuba daga zunubansu, sai Yahaya ya yi masu baftisma. Shugabanin addini da yawa suka zo wurin Yahaya domin ya yi masu baftisma, amma basu tuba ko kuma su furta zunubansu ba.
Yahaya ya ce wa shugabanin addinin, "Ku macizai masu dafi! Ku tuba ku sake halayen ku. Duk itacen da bata bada 'ya'ya mai kyau ba, za a sare ta a jefa ta cikin wuta." Yahaya ya cika abin da annabawa suka fada, "Duba, na aiko manzo na, a yariga ka gaba, wanda zai shirya hanyar ka."
Wassu daga cikin Yahudawan suka tambayi Yahaya ko shi ne Almasihu, Yahaya kuwa ya amsa, "Bani ne Almasihun ba, amma akwai wanda ke biye da ni. Shi mai girma ne, wanda ban isa in kwance takalmansa ba.''
Kashe gari, Sai Yesu yazo domin Yahaya ya yi masa baftisma. Da Yahaya ya ganshi, sai ya ce, "Duba! Ga 'Dan Rago na Allah wanda zai kawar da zunuban duniya."
Yahaya ya ce wa Yesu, "Ban isa in yi maka baftisma ba. Maimakon haka kaine zaka yi mani baftisma.'' Amma Yesu yace, ''Kayi mani baftisma, domin abin da ya dace ne ayi." Hakanan Yahaya ya yi masa baftisma, ko da shike Yesu bai taba yin zunubi ba.
Sa'anda Yesu ya fito daga ruwa, bayan an yi masa baftisma, sai Ruhun Allah ya bayyana a misalin kurciya ya sauko a kansa. A wannan lokaci, muryar Allah yayi magana daga sama, yana cewa, "Kai 'Da na ne wanda nake kauna, ina kuma farin ciki da kai sosai."
Allah ya fadawa Yahaya, "Ruhu Mai Tsarki zai sauko kan wani wanda zaka yi masa baftisma. Wannan mutumin shi ne 'Dan Allah." Allah daya ne. Amma da Yahaya ya yi wa Yesu baftisma, ya ji Allah Uba yayi magana, ya ga Allah 'Da, shi ne Yesu, ya kuma ga Ruhu Mai Tsarki.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 3; Markus 1:9 -11; Luka 3:1-23
Nan da nan bayan an yi wa Yesu baftisma, Ruhu Mai Tsarki ya bishe Yesu zuwa jeji, in da ya yi azumi kwanaki da dare arba'in, sai Shaidan ya zo wurin Yesu ya jarabce shi domin ya yi zunubi.
Shaidan ya jarabci Yesu yana cewa, in kai ne dan Allah, ka mai da duwatsun nan gurasa, don ka ci
Yesu amsa ya ce, "A rubuce ya ke a kalmar Allah, 'Mutane basu bukatar gurasa kawai don su rayu, amma suna bukatar kowace kalma da Allah yake fada!"'
Sa'annan Shaidan ya dauki Yesu ya kai shi saman haikali a wurin da ya fi tsawo duka, ya ce masa, "In kai ne dan Allah ka yi tsalle daga nan zuwa kasa, domin a rubuce yake, 'Allah zai umurci mala'ikunsa su tallafe ka domin kada kafanka ya yi tuntube da dutse.'''
Amma Yesu ya amsa wa Shaidan da abinda aka rubuta daga cikin Nassi. Ya ce, "A kalmar Allah, ya umurci mutanensa, 'Kada ku gwada Ubangiji Allahn ku."'
Sai Shaidan ya nuna wa Yesu dukkan mulkokin duniya da dukkan daukakarsu kuma ya ce, "Zan baka dukkan wannan, idan ka rusuna ka yi mani sujada."
Yesu amsa "Rabu da ni, shaidan! A kalmar Allah ya umurci mutanensa, 'Ku yi wa Ubangiji Allahn ku sujada shi kadai kuma za ku bauta wa"'
Yesu bai fada cikin jerabobin Shaidan ba, saboda haka Shaidan ya rabu da shi. Sai mala'iku suka zo suka yi wa Yesu hidima.
Labari a Littafi Mai Tsarki Daga: Matiyu 4:1-11; Markus 1:12-13; Luka 4:1-13
Bayan ya yi nasara da jarabobin Shaidan, Yesu ya dawo cikin ikon Ruhu Mai Tsarki zuwa yankin Galili inda ya zauna. Yesu ya tafi wurare dabam dabam yana koyarwa. Kowa ya fadi abu mai kyau game da shi.
Yesu ya tafi garin Nazaret, in da ya zauna yayi yarantakar sa. A ranar Asabar ya tafi masujada. Sai aka mika mashi littafin annabi Ishaya domin ya karanta daga ciki. Yesu ya bude littafin ya kuma karanta wa mutane daga wani sashi.
Yesu yayi karatu, "Allah ya bani Ruhun sa, domin in yi shailar bishara ga talakawa, 'yanci ga daurarru, gani ga makafi, saki ga wadanda aka danne. Wannan ita ce shekarar alheri ta Ubangiji."
Sa'annan Yesu ya zauna. Kowannen su, suka zuba masa ido sosai. Suna sane da sashin nassin da ya karanta na magana ne game da Almasihu. Yesu ya ce, "Kalmonin da na karanta maku suna faruwa yanzu.'' Dukkan mutanen suka yi mamaki. Suka ce, ''Ashe wannan ba 'dan Yusufu bane?''
Sa'annan Yesu ya ce, "Gaskiya ne,ba annabin dake samun karbuwa a garinsa. A lokacin annabi Iliya akwai gwauraye da yawa a Isra''ila. Amma da ba'a yi ruwan sama na shekaru uku da rabi, Allah bai aiki Iliya ya taimaki wata gwauruwa daga Isra'ila ba, amma ya ga wata gwauruwa daga wata al'umma dabam."
Yesu ya ci gaba da cewa, "A lokacin annabi Ilisha, akwai mutane da yawa masu cututtukar fata. Amma Ilisha bai warkar da ko dayansu ba. Ya warkar da cutar fatar Na'aman kadai, shugaban rundunar magabtan Isra'ila.'' Mutanen dake sauraron Yesu Yahudawa ne. Da suka ji ya ce haka, sai suka husata sosai akan sa.
Mutanen Nazaret suka ja Yesu daga masujadar, suka kai shi karshen wani tudu domin su jefar dashi da niyyar su kashe shi. Amma Yesu ya ratsa ta tsakiyar su ya bar garin Nazaret.
Sa'annan Yesu ya bi dukkan yankin Galili, taron jama'a suka zo wurin sa. Suka kawo mutane dayawa marassa lafiya, nakasassu, tare da makafi, da guragu, kurame, da bebaye, sai Yesu ya warkar da su.
Aka kawo wa Yesu mutane da yawa masu aljannu. Ta wurin umarnin Yesu, aljannun suka fita daga cikin mutanen, yawancin lokaci sukan yi ihu, ''Kai 'Dan Allahne!'' Taron mutanen suka yi mamaki, suka yi wa Allah sujada.
Sa'annan Yesu ya zabi mazaje goma sha biyu, wadanda ya kira su manzannin sa. Manzannin suka yi tafiya tare da Yesu suna koya daga gare shi.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 4:12-25, Markus 1:14-15, 35-39; 3: 13-2, Luka 4:14-30, 38-44
Wata rana, wani masanin shari'ar Yahudawa, ya zo wurin Yesu domin ya gwada shi, yana cewa, "Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?" Yesu ya amsa, "Me aka rubuta a shari'ar Allah?"
Gwanin a dokokin Allah ya ce, "Ku kaunaci Ubangiji Allahn ku da dukkan zuciyar ku, da ran ku, da karfin ku, da kuma hankalin ku. Ka kuma kaunaci, makwabcin ka kamar kanka." Yesu ya amsa, "Ka yi dai dai! Ka yi haka za ka rayu."
Amma masanin shari'ar ya so ya tabbatar shi mai adali ne, sai ya sake yin tambaya, "Wanene makwabci na?"
Yesu ya amsa wa masanin shari'ar ta wurin bada labari. "An yi wani Bayahude da yake tafiya akan hanya daga Urushalima zuwa Yariko."
"Yayin da mutumin yake tafiya, 'yan fashi suka fada masa. Suka kwace duk abin da ye ke da shi, suka kuma yi masa duka har ya kusa mutuwa. Sa'anna suka yi tafiyar su."
"Nan da nan bayan haka, wani Firist Bayahude tafiya ta kawo shi wannan hanyar. Da wannan shugaban adini ya ga mutumin da aka yi wa duka da fashi, sai ya bi gefe daya na hanyar, ya kyale mutumin nan dake bukatar taimako, ya ci gaba da tafiya.''
"Jim kadan da yin haka, wani Balawe ya gangaro kan hanyar. (Lawiyawa sune kabilun Yahudawa wandanda ke taimakon firistoci a Haikali.) Balawen shima ya ketare gefen hanya, bai kula mutumin da haka yi wa fashi da duka ba."
"Mutumin da ke biye akan hanyar kuwa Basamare ne. (Samariyawa sune zuriyar Yahudawa wadan da suka auri mutane daga wassu al'umma. Samariyawa da Yahudawa sun tsani juna.) Amma da Basamaren ya ga Bayahuden, ya yi juyayi domin sa. Sai ya lura da shi ya daure masa raunukansa."
"Basamaren ya dauki mutumin nan ya sa akan jakin sa, ya kai shi wani masauki baki kusa da hanya inda ya kula da shi."
Kashegari, Basamaren yana bukatar yaci gaba da tafiyar sa. Sai ya ba wa mai kula da masaukin kudi yace, 'Ka lura da shi, idan kudin da kashe yafi wannan, zan biya ka idan na dawo.'''
Sa'annan Yesu ya tambayi masanin shari'ar, "Me kake tunani? A cikin mutanen nan uku, wanene makwabcin wanda aka yi wa fashi da duka?" Sai ya amsa. "Wanda ya yi masa jinkai." Yesu ya gaya masa, "Kaima jeka kayi haka."
Labari a Littafi mai Tsarki daga: Luka 10:25-37
Wata rana, wani saurayi mai arziki shugaba ya zo wurin Yesu, ya yi masa tambaya, "Malam Managarci me zan yi domin in sami rai madawwami?'' Yesu ya ce masa, ''Don me ka kira ni 'managarci'? Managarci daya ne, shine Allah. Amma Idan kana so ka sami rai madawwami, kayi biyayya da dokokin Allah.''
Yayi tambaya, ''Wadanne ne nake bukata in yi biyayya da su?'' Yesu ya amsa, ''Kada ka yi kissan kai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi karya. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, sannan ka kaunaci makwabcin ka kamar yadda ka ke kaunar kanka.''
Amma saurayin ya ce, ''Na yi biyayya da dukkan wadannan dokokin tun ina dan yaro. Me nake bukata kuma in yi domin in rayu har'abada?'' Yesu ya kalle shi ya kaunace shi.
Yesu ya amsa, ''Idan kana so ka zama cikakke, to, ka je ka sayar da dukkan mallakar ka, ka ba wa talakawa kudin, za ka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni.''
Da saurayin ya ji abin da Yesu ya fada, sai ya cika da bakin ciki, domin shi mai arziki ne sosai, kuma bai so ya ba da dukkan mallakarsa ba. Sai ya juya ya tafi daga wurin Yesu.
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, "Yana da wuya kwarai ga mutane masu arziki su shiga mulkin Allah! I, ya fiye sauki rakumi ya shiga ta ramin allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.''
Sa'anda almajiran suka ji abin da Yesu ya fada, sai suka yi mamaki suka ce, "To wanene zai sami ceto?''
Yesu ya dubi almajiran , ya ce, ''Ga mutane wannan ba shi yiwuwa, amma da Allah kome mai yiwuwa ne.''
Bitrus ya ce wa Yesu, ''Mun bar kome mun bi ka, me zai zama sakamakon mu?''
Yesu ya amsa, ''Duk wanda ya bar gidaje, 'yan'uwa maza, da mata, uba da uwa, da 'ya'ya ko mallaka saboda ni, zai sami sama da ribi 100, ya kuma sami rai madawwami. Amma dayawa dake na farko za su zama na karshe, kuma wadanda ke na karshe za su zama na farko.''
Labari a Lttafi Mai Tsarki daga: Matta 19:16-30; Markus 10:17-31; Luka 18:18-30
Wata rana, Bitrus ya tambayi Yesu, "Maigida, sau nawa zan yafe wa dan'uwa na, idan yayi mani laifi? Har sau bakwai?'' Yesu ya ce, "Ba sau bakwai ba, amma saba'in sau bakwai!" Ta haka Yesu, na nufin mu rika yafewa a kowone lokaci. Daga nan Yesu ya bada wannan labarin.
Yesu ya ce, "Mulkin Allah na kama da wani sarki wanda yana son ya daidaita ajiyarsa da barorinsa. Daya daga cikin barorin sa na da bashi mai yawan kimanin albashin shekara 200,000."
"Tunda baran ba zai iya biyan bashinsa ba, sarkin ya ce, 'Ku sayar da mutumin nan da iyalinsa su zama bayi don a sami kudin biyan bashin sa."'
"Baran ya fadi kan gwiwarsa a gaban sarkin ya ce, 'Ka yi mini hakuri zan biya ka dukkan kudin ka da yake na.' Sarkin ya ji tausayin baran, ya share duk bashin sa ya sake shi, ya tafi."
"Amma da baran nan ya fita daga wurin sarkin, ya ga wani bara dan'uwan sa da yake binsa bashi na misallin albashin wata hudu. Baran nan ya damke dan'uwan sa ya ce, 'Ka biya ni kudin da nake binka!'"
"Dan'uwan sa baran ya fadi akan gwiwar sa, ya ce, 'Ka yi hakuri da ni, zan biya dukkan kudin da kake bi na.' Amaimakon haka baran nan ya jefa dan'uwan sa, kurkuku sai lokacin da zai iya biyan duk kudin da yake binsa."
"Da wasu barorin sun ga abinda ya faru suka damu kwarai. Suka je wurin Sarki suka gaya masa abin da ya faru."
"Sarkin ya kira baran ya ce, 'Kai mugun bara! Na yafe maka bashin ka, don ka rokeni. Ai da kaima kayi masa haka.' Sarki ya yi fushi ya kama bawan ya jefa mugun bawan cikin kurkuku har sai ya iya biyan duk kudin da yake bin sa."
Sa'annan, Yesu ya ce, "Haka Ubana na sama zai yi wa kowane dayan ku, idan ba ku yafe wa dan'uwan ku daga cikin zuciya ba."
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta. 18: 21-35
Yesu ya aiki manzaninsa su yi wa'azi da koyarwa a kauyuka dabam-dabam masu yawa. Da suka dawo, wurin da Yesu yake, suka gaya masa abin da suka yi. Sai Yasu ya gayyace su, su je wani wuri tare da shi a kebe a ketaren tafki domin su huta a can na dan lokaci. Sai, suka shiga jirgin ruwa suka ketare zuwa gaccin tafkin.
Amma akwai mutane da yawa da suka ga Yesu da almajiran sa sun tafi a jirgin ruwan. Wadannan mutanen suka ruga suka bi bakin tafkin domin su riga su zuwa dayan tsallaken. Yayin da Yesu da almajiran sa suka isa can, taron mutane da yawa na nan suna jiran su.
Taron na da maza fiye da 5,000, ba a ma kirga mata da yara ba. Yesu ya yi juyayi kwarai game da mutanen. Ga Yesu, mutanen nan na kama suke da tumaki da basu da makiyayi. Saboda haka ya koyar da su, ya kuma warkar da wadan da suke da rashin lafiya a cikin su.
Can da yamma, almajiran suka ce wa Yesu, "Lokaci ya kure kuma ba garuruwa kusa. Ka sallami mutanen domin su je su sami abinda za su ci."
Amma Yesu ya ce wa almajiran, "Ku ba su abinda za su ci!" Suka ansa da ce wa, "Ya ya zamu yi haka? Muna da curin gurasa biyar da 'yan kifi biyu."
Yesu ya ce wa almajiran sa, su ce wa mutanen dake taron su zauna a kan ciyawa, a rukunin mutane hamsin hamsin.
Sa'annan Yesu ya dauki gurasa biyar da kifi biyun, ya duba sama, ya kuma godewa Allah domin abincin.
Sai, Yesu ya gutsuttsura gurasar da kifin. Ya ba wa almajiran sa, don su ba wa mutanen. Almajiran su ka ci gaba da mika abincin, bai kuma kare ba! Dukkan mutanen suka ci suka kuma koshi.
Bayan haka, almajiran suka tattara sauran abincin da ba'a ci ba, ya kuma isa ya cika kwanduna goma sha biyu! Dukkan abincin nan ya samu ne daga gurasa biyar da kifi biyun.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 14:13-21; Markus 6:31-44; Luka 9:10-17; Yahaya 6:5-15
Sa'annan Yesu ya fada wa almajiransa su shiga jirgin ruwa su haye zuwa wancan gefen tafki sa'adda da ya tsaya ya sallami taron. Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya haura gefen tsauni domin ya yi addu'a. Yesu na wurin nan shi kadai, ya kuma yi addu'a har zuwa kurewar dare.
A wannan lokaci, almajiran na tukin jirgin ruwansu, amma a kurewar daren, sun kai tsakiyar ruwan ne kawai. Suna tuki da wahala, domin iska na hurawa da karfi gaba da su sosai.
Sa'annan Yesu ya gama addu'a sai ya tafi wurin almajiran. Yayi tafiya akan ruwa yana haye tafkin zuwa wurin jirgin su!
Almajiran suka tsorata kwarai da suka ga Yesu, domin a tunaninsu fatalwa suke gani. Yesu ya san cewa tasorace suke, sai ya kira su, ya ce, "Kada ku ji tsoro. Ni ne!"
Sai Bitrus ya ce wa Yesu, "Ya shugaba, idan dai kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka a kan ruwan." Yesu ya ce wa Bitrus, "Zo!"
Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwar ya fara tafiya zuwa wurin Yesu a kan ruwa. Amma da yayi tafiya kadan, sai ya kau da idanunsa daga Yesu ya fara duban rakuman ruwa, yana jin yadda kakkarfar iskar take.
Sai Bitrus ya ji tsoro ya kuma fara nutsewa a ruwa. Sai yayi kuka, "Ya shugaba, ka cece ni!" Nandanan Yesu ya isa wurin sa ya kama shi. Sa'annan ya ce wa Bitrus, "Kai mutum mai karamin bangaskiya, me ya sa ka yi shakka?"
A lokacin da Bitrus da Yesu suka shiga jirgin ruwan, nan da nan iskar ta dena kadawa, ruwan kuma ya natsu. Almajiran suka yi mamaki. Suka yi wa Yesu sujada, suna cewa, "Gaskiya, kai Dan Allah ne."
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 14:22-33; Markus 6:45-52; Yahaya 6:16-21
Wata rana, Yesu da almajiransa suka ketare tafki a cikin jirgin ruwa zuwa wa lardin da mutanen Garisinawa ke zama.
Da suka kai daya bangaren tafkin, sai wani mutum da aljannu suka mallake shi ya rugo a guje zuwa wurin Yesu.
Wannan mutum yana da karfi sosai, har ma babu mai ikon bi da shi. Har ma mutane sun sa masa sarka a hannaye da kafafu, amma ya yi ta tsintsinke su.
A makabarta mutumin yake zama. Mutumin yakan yi kururuwa dukan dare da dukan rana. Ba ya sa tufafi yana ta yanka jikinsa da duwatsu kullum.
Da mutumin ya zo wurin Yesu, sai ya fadi a gwiwarsa a gaban sa. Yesu ya ce wa aljannin, "Fita daga cikin wannan mutumin!"
Mutumin nan mai aljanni yayi kuka da murya mai karfi, "Me kake so da ni, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka kada kayi mani azaba." Sai Yesu ya tambayi aljannin, "Menene sunan ka?" Ya amsa, "Suna na Tuli, domin muna da yawa." ("Tuli" jimla ce ta rundunar sojoji dubun dubbai na mayakan Romawa.)
Aljannun suka roki Yesu, "Muna rokonka kada ka kore mu daga wannan lardin!'' Akwai wani garken aladu da ke kiwo a wani tudu kusa da wurin. Sai, aljannun suka roki Yesu, "A maimakon haka ka tura mu cikin aladun nan in ka yarda!" Yesu ya ce, "Tafi!"
Aljannun sun fita daga mutumin sun shiga cikin aladu. Aladun kuwa suka ruga sai cikin tafki, a inda suka hallaka. Garken aladun kuwa sun kai 2,000.
Da makiyan aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga cikin gari, suka gaya wa duk wanda suka gani abin da Yesu ya yi. Mutanen garin suka fito, suka ga mutumin da ke da aljannu a da. Yana zaune a natse, yana cikin hankalinsa, yana kuma sanye da tufafi.
Mutanen sun ji tsoro kwarai, sun roki Yesu ya rabu da su. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa da shirin tafiya. Mutumin da ke da aljannun a da, ya roka ya tafiya tare da Yesu.
Amma Yesu ya ce masa, "A'a, Ina so ka je gida ka fada wa abokan ka da iyalin ka dukan abin da Allah yayi maka, da kuma yadda ya nuna maka jinkai."
Mutumin ya tafi, ya kuma fada wa kowa da kowa abin da Yesu yayi masa. Duk wanda ya ji labarinsa, ya cika da mamaki da al'ajibi.
Yesu ya koma wancan bangare na tafkin. Da isowarsa can, taron jama'a masu yawa suka taru kewaye da shi, suka matse shi. A taron jama'ar kuwa, akwai wata mace wanda ta wahala sosai da damuwa na zubar da jini har na shekaru goma-sha-biyu. Ta kashe kudin ta duka wurin likitoci don su warkar da ita, amma damuwar sai kara muni yayi.
Ta ji cewa Yesu ya warkar da marasa lafiya da yawa, a cikin tunaninta ta ce, "Na tabbata idan har na iya taba tufafin Yesu kawai, ni ma zan warke!" Sai ta zo ta bayan Yesu, ta taba tufafin sa. Da zaran ta taba su, sai zuban jinin ya tsaya!
Nan da nan, Yesu ya gane da cewa iko ya fita daga gareshi. Sai ya juya yayi tambaya, "Wa ya taba ni?" Almajiran suka amsa, "Mutane da yawa ke anan, gasu nan kewaye da kai har turin ka suke yi. Me ya sa ka yi tambaya, 'Wa ya taba ni?'"
Macen nan ta fadi a kan gwiwowinta a gaban Yesu, tare da tsoro da rawan jiki. Sai ta fada masa abin da ta yi, da kuma cewa ta sami warkaswa. Yesu ya ce ma ta, "Bangaskiyar ki ya warkar da ke. Ki tafi cikin salama."
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 8:28-34; 9:20-22; Markus 5:1-20; 5:24b-34; Luka 8:26-39; 8:42b-48
Wata rana, Yesu na koyar da taro mai yawan gaske kusa da bakin tafki. Sai mutane da yawa suka zo su saurare shi, har Yesu ya shiga jirgin ruwa a iyakan ruwan domin dai ya sami sarari yayi magana da su. Ya zauna cikin jirgin ya koyar da mutanen.
Yesu ya fadi wannan labari. "Wani manomi ya tafi ya shuka wassu iri. Da yake watsar da irin da hannu, wassu irin suka fada a kan hanya, tsuntsaye kuma sun zo suka tsince irin duka."
"Wassu irin kuma sun fada a cikin duwatsu, inda babu kasa sosai. Irin da ke cikin duwatsun suka tashi da sauri, amma saiwarsu basu iya shiga da zurfi cikin kasa ba. Da rana ya taso yayi zafi, shukin suka yankwane suka mutu."
"Har yanzu wassu irin suka fada tsakanin kayayuwa. Irin nan suka fara yin girma, amma kayayuwa suka shake su. Saboda haka shukin da suka yi girma daga irin nan da aka shuka cikin kayayuwa basu ba da wani kwaya ba."
"Wassu iri kuwa suka fada a cikin kasa mai kyau. Irin nan suka yi girma, suka kuma ba da amfani ribi 30, 60, har ma 100 kamar yawan iri da aka shuka. Mai kunnen ji, ya ji!"
Wannan labarin ya rikitar da almajiran. Saboda haka Yesu ya bayyana, "Irin nan kalmar Allah ne. Hanyan nan kuma mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, amma bai gane ba, sai shaidan ya dauke kalmar daga gareshi."
"Kasa mai duwatsun nan kuma, mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, ya kuma karbe shi da murna. Amma da ya da ji wahala ko tsanani, sai ya fadi."
"Kasa mai kayayuwa, mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, amma da lokaci na wucewa, kwadayin kayan duniya, arziki, da kuma anashuwa na wannan rayuwa suka shake kaunar Allah a cikin sa. Sakamakon haka, koyarwa da ya ji bai ba da 'ya'ya ba."
"Amma kasa mai kyau, mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, ya gaskanta shi, ya kuma ba da 'ya'ya."
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 13:1-8, 18-23; Markus 4:1-8, 13-20; Luka 8:4-15
Yesu ya fadi wadansu labaru da yawa game da Mulkin Allah. Misali, yace, "Mulkin Allah kamar kwayar mastad ya ke da wani ya shuka a gonarsa. Kun sani cewa kwayar mastad ita ce mafi kankanta dukka cikin iri."
"Amma sa'anda kwayar mastad ya girma, sai yafi dukkan itatuwan dake gona girma, kuma da girma sosai harma tsuntsaye sukan zo su huta a cikin rassan sa."
Yesu ya sake fadin wani labari, "Za'a kwatanta mulkin Allah da yistin da mace ke kwabawa cikin curin gurasa har sai ya mamaye dukka curin."
Haka kuma mulkin Allah kamar dukiya ce da wani ya boye a wani fage. Wani mutum dabam ya sami dukiyar shi ma ya sake binne ta. Yana cike da murna harma ya je ya sayar da dukkan mallakar sa, ya yi amfani da kudin don ya sayi filin."
"Haka kuma mulkin Allah kamar lu'u lu'u ne mai darajar gaske. Sa'anda dillalin lu'u lu'u ya same ta, sai ya sayar da dukkan mallakar sa ya yi amfani da kudin domin ya saye ta.''
Sa'annan Yesu ya fadi wani labari wa mutane da suke dogara da ayyukan su nagari amma su na raina sauran mutane. Yace, "Mutane biyu suka je haikali don su yi addu'a. Daya mai karbar haraj i ne, dayan kuma shugaban addini ne."
"Shugaban addinin yayi addu'a kamar haka, 'Na gode maka Allah, domin ni ba mai zunubi bane kamar sauran mutane, barayi, marasa adalci, mazinata, ko kuma kamar wancen mai karban haraji.'''
'''Misali, na kan yi azumi sau biyu ko wace mako, nakan kuma baka daya bisa goma cikin dukkan kudi da kayayyakin da na karba."'
"Amma mai karbar harajin ya tsaya nesa da shugaban addini, baya ma duban sama. A maimakon haka, ya dunkula hannu yana buga girjinsa ya yi addu'a, 'Allah, yi mani jinkai domin ni mai zunubi ne.'''
Sai Yesu yace, "Gaskiya nake gaya maku, Allah ya ji addu'ar mai karban harajin nan ya kuma ce da shi adali. Amma bai so addu'ar shugaban addinin nan ba. Allah zai kaskantar da duk mai fahariya, ya kuma daukaka duk wanda ya kaskantar da kansa."
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 13:31-33, 44-46; Markus 4:30-32; Luka 13:18-21; 18:9-14
Wata rana, Yesu na koyar wa, masu karbar haraji masu yawa da wadansu masu zunubi suka taru domin su saurare shi.
Wadansu shugabannin addini dake wurin suka ga Yesu yana ma'amala da masu zunubi a matsayin abokai, sai suka fara zargin sa a tsakansu. Sai Yesu ya fada masu wannan labari.
"Akwai wani mutum wanda yake da 'ya'ya biyu. Karamin dan ya ce wa Ubansa, 'Baba, ina son rabon gado na yanzu!' Sai uban ya raba dukiyarsa tsakanin 'ya'yan guda biyu."
"Bada jimawa ba sai karamin dan ya tara dukkan abinda yake da shi ya tafi da nisa ya barnatar da kudin sa cikin rayuwar zunubi."
"Bayan haka, aka yi fari mai tsanani a kasar da karamin dan yake, kuma bashi da kudin sayan abinci. Sai ya karbi aiki da ya samu, na ciyad da aladu. Ya zamana da bakin ciki kuma ga yunwa har ma yana so ya ci abincin aladu."
"'A karshe, karamin dan yace wa kansa, 'Me nake yi? Dukkan barorin ubana suna da abinci da yawa, amma gani nan ina fama da yunwa. Zan koma gun ubana in roke shi in zama daya daga cikin barorin sa."'
"Sai karamin dan ya kama hanyar zuwa gidan uban sa. Tun yana nesa, uban ya hango shi ya ji tausayin sa. Ya ruga zuwa wurin dansa ya kuma rungume shi ya sumbace shi."
"Dan yace, 'Baba, na yi wa Allah zunubi na kuma yi maka. Ban cancanci in zama dan ka ba.'"
"Amma ubansa yace wa daya daga cikin barorinsa, 'Je ka da sauri ka kawo tufafi mafi kyau ka sa wa dana! Ka sa zobe a yatsarsa ka kuma sa takalma a kafafunsa. Sai ka yanka dan maraki mafi kyau, domin mu yi bukin farin ciki, domin dana ya mutu, amma yanzu ya rayu! Ya bata, amma yanzu an same shi!"'
"Sai mutanen suka fara bukki. Bada jimawa ba, sai ga babban dan ya dawo gida daga aiki a goma. Ya ji kide-kide da raye-raye, ya yi tunanin me ke faruwa."
"Sa'anda babban dan ya gane cewa ana bukki domin dan'uwansa ne ya komo gida, sai ya husata kuma yaki shiga gidan. Ubansa ya fito ya roke shi ya shigo yayi bukin dasu, amma ya ki."
"Sai babban dan yace wa ubansa, 'Dukkan shekarun nan nayi maka aiki da aminci! Ban taba yi maka rashin biyayya ba, duk da haka baka bani ko dan akuya in yi buki da abokaina ba. Amma sa'adda wannan dan naka wanda ya batar da kudinka cikin aikin zunubi ya komo gida, ka yanka dan maraki mafi kyau domin sa!'"
"Sai uban ya amsa, 'Dana, kana tare dani kullum, kuma dukkan abinda nake dashi naka ne. Amma daidai ne muyi buki, domin dan'uwanka ya mutu, amma yanzu yana raye. Ya bata, amma yanzu an same shi!'"
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Luka 15:11-32
Wata rana, Yesu ya dauki uku daga cikin almajiransa, Bitrus, Yakubu, da Yahaya. (Almajirin nan mai suna Yahaya ba shine wanda yayi wa Yesu baftisma ba.) Sun hau kan dutse mai tsawo domin su yi addu'a su kadai.
Da Yesu yana addu'a, sai fuskarsa tayi annuri (Haske) kamar rana kuma tufafinsa suka zama fari fat, fiye da yadda wani a duniya zai maishe su.
Sa'annan Musa da annabi Iliya suka bayyana. Wadannan mutane sun yi zama a duniya daruruwan shekaru kafin lokacin nan. Sun yi magana da Yesu game da mutuwarsa, wanda zai faru ba da dadewa ba a Urushalima.
Yayin da Musa da Iliya ke magana da Yesu, Bitrus yace wa Yesu, "Yana da kyau da muke a nan. Bari mu kafa bukkoki uku, daya na ka, daya na Musa, daya kuma na Iliya." Bitrus bai san abinda yake fada ba.
Yayin da Bitrus ke magana, girgije mai haske ta sauko ya lullube su sai murya daga girgijen ya ce, "Wannan shine dana wanda nake kauna. Ina farin ciki da shi. Ku saurare shi." Almajiran nan uku suka razana suka fadi kasa.
Sai Yesu ya taba su ya ce, "Kada ku ji tsoro. Ku tashi." Sa'anda suka duba kewaye, sai Yesu shi kadai ke wurin.
Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga dutsen. Sai Yesu yace masu, "Kada ku gaya wa kowa abinda ya faru anan tukunna. Bada dadewa ba, zan mutu in kuma sake rayuwa. Bayan haka, zaku iya fada wa mutane."
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 17:1-9; Markus 9:2-8; Luka 9:28-36
Wata rana, Yesu ya sami sako cewa Li'azaru yana tsananin rashin lafiya. Li'azaru da yan'uwansa biyu mata, Maryamu da Marta, abokan Yesu ne na kusa. Sa'anda Yesu ya ji labarin, sai ya ce, "Wannan ciwon ba zai kare a mutuwa ba, amma domin daukakar Allah." Yesu ya na kaunar abokansa, amma ya jira har kwana biyu a inda ya ke.
Bayan kwana biyun sun wuce, Yesu ya ce wa almajiransa, "Bari mu koma Yahudiya." Almajiran suka amsa, ''Amma malam, ba da dadewa ba mutanen wurin sun so su kashe ka!" Yesu ya ce, "Abokin mu Li'azaru ya yi barci, kuma dole ne in tashe shi."
Almajiran Yesu suka amsa, "Mai gida, inda Li'azaru ya na barci, to ya zama masa mafi alheri." Sa'annan Yesu ya gaya masu afili, "Li'azaru ya mutu. Na yi murna da ba na nan a wurin, domin ku gaskanta da ni."
Sa'adda Yesu ya isa garin Li'azaru, Li'azaru ya riga ya mutu da kwana hudu. Marta ta fito waje ta sami Yesu, ta ce, "Maigida, inda kana nan, da dan'uwana bai mutu ba. Amma na gaskanta Allah zai ba ka duk abinda ka roka daga gare shi."
Yesu ya amsa, "Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskanta da ni zai rayu, ko da ma ya mutu. duk wanda ya gaskanta da ni ba zai taba mutuwa ba. Kin gaskanta da wannan?" Marta ta amsa, "I, Maigida! Na gaskanta kai ne Almasihu, Dan Allah."
Sa'annan Maryamu ta iso. Ta fadi a kaffafun Yesu, ta ce, "Maigida, da dai kana nan, da dan'uwana bai mutu ba." Yesu ya tambaye su, "Ina ku ka ajiye Li'azaru?" Suka gaya masa, "A kabari. Zo ka gani." Sa'annan Yesu ya yi kuka.
Kabarin kogo ne, da dutse da aka mirgina a gaban kofar. Sa'anda Yesu ya isa kabarin, ya gaya masu, "Ku mirgina dutsen." Amma Marta ta ce, "Kwana hudu ke nan da mutuwarsa. Za a yi mummunar wari."
Yesu ya amsa, "Ba na gaya ma ki cewa za ki ga daukakar Allah idan ki ka gaskanta ni ba?" Sai suka mirgina dutsen gefe.
Sai Yesu ya dubi sama ya ce, "Uba, na gode maka domin kana ji na. Na san ka na ji na kullum, amma na fadi haka saboda wadannan mutane da ke tsaye a nan, domin so bada gaskiya kai ka aiko ni." Sai Yesu yayi ihu, "Li'azaru, fito wuje!"
Sai Li'azaru ya fito waje! Yana nannade a likafani. Yesu ya ce masu, "Ku taimake shi cire likafanin ya tafi!" Yahudawa da yawa sun gaskanta da Yesu saboda wannan al'ajibi.
Amma shugabanin adinin na Yahudawan suka ji kyashi, sai suka taru domin su shirya yadda za su kashe Yesu da Li'azaru.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Yahaya 11: 1-46
Kowace shekara, Yahudawa su na bukin idin ketarewa. Wannan buki ne na yadda Allah ya ceci kakaninsu daga bauta a Masar shekaru masu yawa. Wajen shekaru uku bayan Yesu ya fara wa'azi da koyarwa afili, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa ya na so ya yi bikin idin ketarewa da su a Urushalima, za a kuma kashe shi a can.
Daya daga cikin almajiran Yesu wani mutum ne mai suna Yahuza. Yahuza shine mai ajiye jakar kudin Manzanin, amma yana kaunar kudi, wassu lokatai ya kan saci kudi daga jakar. Bayan Yesu da almajiransa suka iso Urushalima, Yahuza ya je wajen shugabanin Yahudawa domin ya bashe da Yesu agare su a maimakon kudi. Ya san cewa shugabanin Yahudawan sun musanci Yesu shine Almasihu kuma suna shawara yadda zasu kashe shi.
Babban firist ya jagoranci, Shugabanin Yahudawan, suka biya Yahuza tsabar azurfa talatin domin ya bashe da Yesu. Wannan ya faru daidai yadda annabawa suka yi anabci. Yahuza ya yarda, ya karbi kudin, ya yi tafiyarsa. Ya fara neman zarafia yadda zai taimake su su kama Yesu.
A Urushalima, Yesu ya yi bikin idin ketarewa da almajiransa. A lokacin abinci idin, Yesu ya dauki gurasa ya gusura shi. Ya ce, "Karba ku ci wannan. Wannan jiki na ne, wanda aka bayar domin ku. Ku yi wannan domin ku tuna da ni." Ta wannan hanya, Yesu yace jikinsa zai zama hadaya domin su.
Sa'annan Yesu ya dauki koko yace, "Sha wannan. Jini na ne na sabon alkawari da aka zubar domin gafarar zunubai. Ku yi wannan don ku tuna da ni a kowane lokaci da ku ke shan sa.
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, "Daya daga cikin ku zai bashe ni." Almajiran suka yi mamaki, sai suka tambaya, wa zai yi irin wannan abu. Yesu yace, "Mutumin da na bashi wannan gutsiren gurasa, shi ne mai bashewa." Sa'annan ya ba wa Yahuza gurasar.
Bayan da Yahuza ya karbi gurasar, Shaidan ya shige shi. Yahuza ya tafi don ya taimaki shugabannin Yahudawan kama Yesu. Da dare ne lokacin.
Bayan abincin, Yesu da almajiransa suka taka zuwa Dutsen Zaitun. Yesu yace, "Dukan ku za ku yashe ni cikin daren nan. A rubuce ya ke, 'Zan bugi makiyayin kuma dukkan tumakin za su watse.'"
Bitrus ya amsa, "Ko da sauran su dukka sun yashe ka, ni ba zan yashe ka ba!" Sai Yesu yace wa Bitrus, ''Shaidan yana so ya rinjaye dukkan ku, amma na yi maku addu'a Bitrus, cewa kada bangaskiyar ku ta kasa. Ko da haka ma, da daren nan, kafin zakara ya yi chara, za ka yi musun sani na sau uku cewa baka ma sanni ba."
Sai Bitrus ya ce wa Yesu, "Ko da ya zama dole in mutu, ba zan yi musun ka ba!" Sai duk sauran almajiran su ma suka ce haka.
Sa'annan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wuri da a ke ce da shi Getsemani. Yesu ya gaya wa almajiransa su yi addu'a domin kada su shiga cikin jaraba. Sa'annan Yesu ya tafi domin ya yi addu'a a kadaice.
Yesu ya yi addu'a sau uku, "Uba, idan zai yiwu, bari kada in sha wannan kokon wahala. Amma idan babu wata hanya da mutane za su sami gafarar zunubai, to bari nufin ka ya tabbata." Yesu ya damu kwarai sai zufar sa ta fara diga kamar jini. Allah ya aiko malai'ika ya karfafa shi.
Bayan kowane lokacin addu'a, Yesu dawo wurin almajiransa, amma suna barci. Sa'anda ya dawo karo na uku, Yesu yace, "Ku tashi! Mai bashe ni ya iso."
Yahuza ya zo da shugabanin Yahudawa, sojoji, da taron jama'a. Suna dauke da takuba da sanduna. Yahuza ya zo wurin Yesu yace, "Gaisuwa, Mallam," ya sumbace shi. Wannan shine alama ga shugabanin Yahudawa domin su san wanda zasu kama. Sai Yesu yace, "Yahuza, ka na bashe ni da sumba?"
Da sojojin suka kama Yesu, Bitrus ya zare takobinsa ya yanke kunnen wani baran babban firist. Yesu yace, "Mayar da takobin ka! Zan iya rokon Uba ya aiko da rundunar malai'iku su kare ni. Amma dole ne in yi biyayya da Ubana." Sa'annan Yesu ya warkar da kunnen mutumin. Bayan da aka kama Yesu, dukkan almajiran suka gudu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 26:14-56; Markus 14:10-50; Luka 22:1-53; Yahaya 12:6; 18:1-11
A tsakiyar dare ne yanzu a wannan lokacin. Sojoji suka kai Yesu a gidan babban firist domin babban firist ya tuhume shi. Bitrus ya bi su daga nesa. Da aka kai Yesu cikin gidan, Bitrus ya tsaya a waje yana jin dumin wuta.
A cikin gidan, shugabannin Yahudawa suka gabatar da Yesu don shari'a. Suka kawo masu shaidar zur da yawa wadanda suka yi karya akansa. Duk da haka, bakinsu bai zo daya ba, don haka shugabannin Yahudawa ba su iya tabbatar da laifin sa ba. Yesu bai ce kome ba.
A karshe, babban firist din ya kafa wa Yesu ido, ya ce, "Gaya mana, ko kai ne Almasihu Dan Allah rayayye?"
Yesu yace, "Ni ne, kuma za ka ganni zaune tare da Allah ina kuma sabkowa daga sama." Babban firist din ya yaga tufaffin sa cikin fushi ya kuma yi ihu ga sauran shugabannin addini, "Ba mu bukatar wassu shaidu kuma! Kun ji shi ya ce shine Dan Allah. Menene hukuncin ku?"
Shugabannin Yahudawan dukka suka amsa wa babban firist din, "Ya cancanci mutuwa!" Sai suka rufe wa Yesu idanu, suka tofa masa yawu, suka buge shi, suka kuma yi masa ba'a.
Yayinda Bitrus yana jira a waje da gidan, wata baiwar yarinya ta gan shi ta kuma ce masa, "Kai ma tare da Yesu ka ke!" Bitrus ya yi musun haka. Daga baya, wata yarinya ta sake maimaita maganar, Bitrus ya sake yin musu kuma. A karshe, mutanen suka ce, "Mun sani cewa tare da Yesu kake domin dukkan ku daga Galili ku ke."
Sai Bitrus ya rantse da cewa, "Bari Allah ya la'anta ni idan na san wannan mutumin!" Nandanan zakara ya yi cara, sai Yesu ya juya ya dubi Bitrus.
Bitrus ya fita yayi kuka mai zafi. A lokacin kuma, Yahuda, maciyin amana, ya ga shugabannin Yahudawa sun yanke wa Yesu hukuncin kisa. Yahuza ya cika da bakinciki ya tafi ya kashe kansa.
Kashegari da sassafe, shugabannin Yahudawa suka kawo Yesu wurin Bilatus, gwamnan Roma. Sun sa zuciya Bilatus zai sami Yesu da laifi ya kuma yanke masa hukuncin kisa. Bilatus ya tambayi Yesu, "Kai ne sarkin Yahudawa?"
Yesu ya amsa, "Haka ka fada, amma mulki na ba na duniya ba. Da haka yake, bayi na zasu yi fada domina. Na zo duniya in fadi gaskiya game da Allah. Duk mai kaunar gaskiya yana sauraro na." Bilatus ya ce, "Menene gaskiya?"
Bayan yayi magana da Yesu, Bilatus ya tafi wurin taron ya kuma ce, "Ban sami laifi a kan wannan mutumin ba." Amma shugabannin Yahudawa da taron suka yi ihu, "Giciye shi!" Bilatus ya amsa, "Ba shi da laifi." Amma suka dada tada murya da karfi. Sai Bilatus ya fada masu karo na uku, "Ba shi da laifi!"
Bilatus ya ji tsoro cewa taron zasu fara tarzoma, sai ya yarda sojojinsa su gicciye Yesu. Sojojin Roma suka yi wa Yesu bulala, suka kuma sanya masa rigar sarauta da rawanin da aka yi ta da kaya a kansa. Sai suka yi masa ba'a suna cewa, "Dubi, Sarkin Yahudawa!"
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 26:57-27:26; Markus14:53-15:15; Luka 22:54-23:25; Yahaya 18:12-19:16.
Bayan sojojin sun yi wa Yesu ba'a, sai suka tafi da shi domin su gicciye shi. Suka sa shi ya dauki gicciyen da zai mutu akai.
Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira, "Kokon kai" suka kafe hannayensa da kafafunsa da kusa akan gicciye. Amma Yesu ya ce, "Uba ka gafarta masu domin basu san abin da suke yi ba." Bilatus ya bada umarni su rubuta, "Sarkin Yahudawa" akan allo su kuma sa shi akan gicciyen, sama da kan Yesu.
Sojojin suka yi kuri'a akan tufafin Yesu. Sa'anda suka yi haka, sun cika wani annabci da ya ce, "Sun raba tufafina a tsakaninsu, suka sa kuri'a akan tufa ta."
Aka gicciye Yesu tsakanin 'yan fashi biyu. Daya daga cikinsu ya yi wa Yesu ba'a, amma dayan ya ce, "Baka da tsoron Allah? mu mun yi laifi amma wannan mutumin bashi da laifi." Sa'anan ya ce wa Yesu, "In ka yarda ka tuna da ni a mulkinka." Yesu ya amsa masa. "Yau zaka kasance tare da ni a fiddausi."
Shugbannin Yahudawa da wadansu mutane a cikin taron suka yi wa Yesu ba'a. Suka ce masa, "Idan kai 'Dan Allah ne sauko daga kan gicciyen ka ceci kanka! sa'annan zamu gaskanta ka."
Sai sararin sama na lardin ya yi baki gaba daya, ko da yake da tsakiyar rana ne. Wuri ya zama duhu da tsakar rana, aka kuma ci gaba da duhu har sa'a uku.
Sa'anan Yesu yi kuka, "Ya kare! Uba na bada ruhu na a cikin hannun ka." Sai ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa. Da ya mutu an yi girgizar kasa, sai babban labulen da ya raba mutane da Allah a Haikali, ya tsage biyu, daga sama zuwa kasa.
Ta wurin mutuwarsa, Yesu ya bude hanya da mutane za su zo gun Allah. Da sojan nan mai tsaron Yesu ya ga dukkan abubuwan da suka faru, sai ya ce, "Hakika, wannan mutumin marar laifi ne. Shi Dan Allah ne."
Sa'annan Yusufu da NIkodimas, shugabannin Yahudawa biyu wadanda suka gaskanta, Yesu Almasihu ne, suka tambayi Bilatus jikin Yesu. Suka nade jikinsa cikin zani suka sa shi cikin kabarin dutse da aka sassaka. Sa'anan suka mirgina babban dutse a bakin kabarin domin su rufe kofar.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 27: 27-61; Markus 15: 16-47; Luka 23:26-56; Yahaya 19: 17-42
Bayan sojajin sun gicciye Yesu, sai shugabannnin Yahudawa marasa bangaskiya suka cewa Bilatus, ''Wannan makaryacin, Yesu, ya ce zai tashi daga matattu bayan kwana uku. Don haka lallai ne wani yayi tsaron kabarin, domin a tabbata cewa almajiran sa ba su saci gangar jikinsa ba, sa'annan su ce ya tashi daga matattu.''
Bilatus yace, ''Ku dauki wassu sojoji kuje ku tsare kabarin gwargwadon iyawarku.'' Sai suka sa hatimi a kan dutsen da ke kofar kabarin da kuma sojoji don su tabbata ba wanda zai iya satar gangar jikin.
Bayan ranar da aka binne Yesu, ranar asabar ce, kuma ba a yardar wa Yahudawa suje kabari a ranar ba. Sai da sassafe bayan asabar, mata da yawa suka yi shiri suje kabarin Yesu, domin su kara zuba turare a gangar jikin sa.
Nan da nan, sai aka yi babbar girgizar kasa. Wani mala'ika mai haske kamar walkiya ya bayyana daga sama.Ya mirgina dutsen dake rufe kofar kabarin gefe guda, ya zauna akai. Sojojin dake tsaron kabarin suka firgita, suka fadi kasa kamar matattun mutane.
Sa'anda matan suka isa kabarin, sai mala'ikan yace masu, "Kada kuji tsoro. Yesu baya nan. Ya tashi daga matattu kamar yadda yace zai yi! Ku duba cikin kabarin ku gani.'' Matan suka duba cikin kabarin inda aka kwantar da jikin Yesu. Babu jikin a wurin!
Sa'annan mala'ikan yace wa matan, ''Kuje ku gaya wa almajiran, 'Yesu ya tashi daga matattu kuma zai riga ku zuwa Galili.'''
Matan suka cika da tsoro da farin ciki. Suka ruga domin su fada wa almajiran wannan labari mai dadi.
Yayin da matan suke hanyar zuwa su fada wa almajiran labarin nan mai dadi, sai Yesu ya bayyana a gare su, sai suka yi masa sujada. Yesu ya ce, ''Kada ku ji tsoro. Ku je ku gaya wa almajiraina su tafi Galili. Zasu gan ni a can.''
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 27:62-28:15; Markus 16:1-11; Luka 24:1-12; Yahaya 20:1-18
A ranar da aka tashi Yesu daga matattu, biyu daga cikin almajiransa na tafiya zuwa wani gari dake kusa. Da suna tafiya, suna magana akan abinda ya faru da Yesu. Sun sa bege cewa shine Almasihu, amma kuma an kashe shi. Yanzu mata sun ce yana da rai kuma. Ba su san abinda zasu gaskanta ba.
Yesu ya zo wurin su, ya fara tafiya da su, amma ba su gane shi ba. Ya tambaye su maganar me suke yi, sai suka gaya masa dukkan manyan abuauwan da suka faru game da Yesu, a 'yan kwanaki da suka wuce. A tunanin su, suna magana ne da wani bako wanda bai san abin da ya faru a Urushalima ba.
Sa'annan Yesu ya bayyana masu abinda maganar Allah ya fadi game da Almasihu. Ya tunashe su cewa annabawa sun ce Almasihun zai sha wahala, a kuma kashe shi, amma zai tashi kuma a rana ta uku. Da suka isa garin da mutanen nan biyu suka yi shirin sauka, yammaci ya kusa.
Mutanen nan biyu su ka gayyaci Yesu ya zauna tare da su, sai ya amince. Sa'anda suka shirya domin cin abincin maraice, Yesu ya dauki curin gurasa, ya gode wa Allah domin ta, ya kuma karya ta. Nandanan, suka gane cewa Yesu ne. A wannan lokaci kuwa, Yesu ya bace daga ganin su.
Sai mutanen biyu suka ce wa juna, "Ai Yesu ne! Shi yasa zuciyar mu take kuna lokacin da ya ke fassara mana maganar Allah!" Nandanan, suka koma Urushalima. Da suka iso, suka fada wa almajiran, "Yesu yana da rai! Mun gan shi!''
Yayin da Almajiran suna cikin magana, nandanan Yesu ya bayyana a cikin dakin tare dasu, sai ya ce, "Salama a gareku!" Almajiran suka yi zaton shi fatalwa ne, amma Yesu yace masu, "Donme kuke jin tsoro kuna kuma shakka? Ku dubi hannaye na da sawaye na. Fatalwa bashi da jiki kamar yadda nake dashi." Domin tabbatar masu shi ba fatalwa ba ne, sai ya roke su wani abu ya ci. Suka ba shi gutsuren dafaffen kifi, sai ya ci.
Yesu ya ce, "Na gaya maku cewa, dukkan abubuwan da aka rubuta game da ni a maganar Allah dole za'a cika su." Sai ya bude fahimtar su domin su iya gane maganar Allah. Ya ce, "A rubuce yake da dadewa cewa Almasihu zai sha wahala, ya mutu, ya kuma tashi daga matattu a rana ta uku."
"An kuma rubuta cikin nassi cewa almajirai na zasu yi shela kowa ya tuba domin ya karbi gafaran zunuban sa. Zasu yi haka da fari cikin Urushalima, sa'annan suje ga dukkan kabilun mutane ko ina. Ku shaidu ne na wadannan abubuwa."
A cikin kwanaki arba'in na gaba, Yesu ya bayyana ga almajiran sa sau dayawa. Wani lokaci ma har ya bayyana ga mutane fiye da 500 lokaci guda! Ya tabbatar wa Almajiransa ta hanyoyi da dama, cewa yana da rai, ya kuma koyar dasu game da mulkin Allah.
Yesu ya ce wa Almajiransa, "An bani dukkan iko a sama da kuma kasa. Saboda haka ku je, ku Almajirantar da dukkan kabilun mutane, ta wurin yi masu baftisma, acikin sunan Uba, da na 'Da, dana Ruhu Mai Tsarki, kuma ta wurin koyar da su, su yi biyayya da dukkan umarnin da Na baku. Ku tuna, Zan kasance da ku kullayomin."
Bayan kwanaki arba'in da tashin Yesu daga matattu, ya ce wa almajiran sa, "Ku zauna a Urushalima har sai Ubana ya ba ku iko, sa'anda Ruhu Mai Tsarki zai sauko a kan ku." Sai Yesu ya tafi sama, sa'annan wani gajimare ya rufe shi daga idanun su. Yesu ya zauna a hannun dama na Allah ya kuma yi mulki bisa dukkan abubuwa.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 28:16-20; Markus 16:12-20; Luka 24:13-53; Yahaya 20:19-23; Ayyukan Manzani 1:1-11
Bayan da Yesu ya koma sama, almajiran suka zauna a Urushalima kamar yadda Yesu ya umarce su su yi. Masu bi a can su kan taru kowane lokaci domin addu'a.
Kowace shekara, kwanaki 50 bayan idin ketarewa, Yahudawa sun kan yi bukin wata muhimmiyar rana da ake kira fentikos, Fentikos rana ce da Yahudawa ke bukin girbin alkama. Yahudawa su kan zo daga ko ina a fadin duniya zuwa Urushalima domin su yi bukin fentikos tare. A wannan shekara, bukin fentikos ya zo ne sati guda bayan Yesu ya koma sama
Sa'adda masu bi dukka suke tare a wuri guda, nan da nan sai gidan da suke ciki ya cika da wani kara kamar iska mai karfi. Sai wani abu kamar harshen wuta ya bayyana a bisa kan dukkan masu bi. Suka cika da Ruhu Mai Tsarki, sai suka fara magana da wadansu harsuna.
Da mutanen da ke cikin Urushalima suka ji hargowar, taron jama'a suka zo su ga abin da ke faruwa. Da suka ji masu bi suna furta ayyukan al'ajibai da Allah ya yi, suka yi mamaki kwarai domin suna jin wadannan abubuwa a harsunansu.
Wadansu daga cikin mutanen suka zargi almajiran cewa a buge suke. Amma Bitrus ya tashi tsaye ya ce masu, ''Ku saurare ni, wadannan mutane ba a buge suke ba! Wannan ya cika annabcin da annabi Yowel ya yi, in da Allah ya ce, 'A kwanakin karshe zan zubo da Ruhu na.'''
"Mutanen Isra'ila, Yesu mutun ne da ya yi manyan alamu da al'ajibai ta wurin ikon Allah, kamar yadda kuka gani kuka kuma sani. Amma kuka gicciye shi."
"Ko da shike Yesu ya mutu, Allah ya tashe shi daga matattu. Wannan ya cika annabcin da ya ce, 'Ba zaka bar Mai Tsarkinka ya rube a kabari ba.' Mu, shaidu ne ga wannan tabbataccen al'amarin nan cewa Allah ya tada Yesu daga matattu."
"An daukaka Yesu yanzu zuwa hannun dama na Allah Uba. Yesu kuma ya aiko Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya alkawarta zai yi. Ruhu Mai Tsarki ne yake sa wadannan abubuwan da kuke gani, kuke kuma ji."
"Kun gicciye mutumin nan, Yesu. Amma ku sani hakika cewa Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu!"
Mutanen da ke sauraron Bitrus suka damu kwarai domin abubuwan da ya fada. Sai suka tambayi Bitrus da almajiran, "Yan'uwa, me za mu yi?"
Bitrus ya amsa masu, ''Kowannen ku ya tuba a kuma yi masa baftisma cikin sunan Yesu Almasihu domin Allah ya gafarta maku zunuban ku. Sa'annan zai baku kyautar Ruhu Mai Tsarki.''
Kimanin mutane 3,000 ne suka gaskanta da maganan da Bitrus ya yi, suka kuma zama almajiran Yesu. Aka yi masu baftisma suka zama 'yan ikkilisiyar da ke Urushalima.
Almajiran suka ci gaba da jin koyarwar manzanni, suna tare kowane lokaci, suna ci tare, suna addu'a tare, suna jin dadin yabon Allah tare, suna yin komai tare, suna kuma rarraba kome da suke da shi tare. Kowa na tunani mai kyau akan su. A kowace rana ana samun karin mutane masu bada gaskiya.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Ayyukan Manzanni 2
Wata rana, Bitrus da Yahaya suna tafiya Haikali. Da suka kusa da kofar shigar Haikalin, suka ga wani gurgu wanda ke rokon kudi.
Biturus ya dubi gurgun ya ce, "Bani da kudin da zan ba ka. Amma zan baka abin da nake dashi. A cikin sunan Yesu, ka tashi ka yi tafiya!"
Nan da nan Allah ya warkar da gurgun, sai ya fara tafiya yana tsalle, ya na yabon Allah. Mutanen da suke harabar Haikalin suka yi mamaki.
Taron jama'a suka zo da sauri don su ga mutumin da aka warkar da shi. Bitrus ya ce masu, "Don me kuke mamakin cewa mutumin nan ya warke? Ba mu warkar da shi da ikon kan mu, ko adalcin mu ba. Maimakon haka, ikon Yesu ne da bangaskiyar da ya bayar ya warkar da mutumin nan."
"Kune wadanda kuka ce wa Gwamnan Roma ya kashe Yesu. Kuka kashe mahaliccin rai. Amma Allah ya tashe shi daga matattu. Ko da yake baku gane abin da kuke yi ba, Allah ya yi amfani da ayyukan ku don Ya cika annabce anabce cewa Almasihu zai sha wahala ya kuma mutu. Saboda haka ku tuba ku juyo ga Allah, domin a wanke zunuban ku."
Shugabannin Haikalin suka husata, da abin da Bitrus da Yahaya suke cewa. Don haka suka kama su, suka sa su cikin kurkuku. Amma mutane da yawa suka gaskanta da sakon da Bitrus ya fada, don haka jimillar mazaje da suka gaskanta da Yesu, ya karu kimanin 5,000.
Washe gari, shugabannin Yahudawa suka kawo Bitrus da Yahaya wurin babban Firist da wassu shugabbannin addini. Suka tambayi Bitrus da Yahaya, "Da wane iko kuka warkar da wannan gurgun mutum?"
Bitrus ya amsa masu, "Wannan mutumin da ke tsaye a gaban ku, ya warke ne ta ikon Yesu Almasihu. Kun gicciye Yesu, amma Allah ya tashe shi da rai! Kuka ki shi, amma ba wata hanyar ceto sai ko ta wurin ikon Yesu!"
Shugabannin suka yi mamaki yadda Bitrus da Yahaya suka yi magana da gabagadi, suna gani su ba kome bane, ba su kuma karantu ba. Amma suka tuna cewa mutanen nan sun kasance tare da Yesu. Bayan da suka tsorata Bitrus da Yahaya, sai suka bar su su tafi.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Ayyukan Manzanni 3: 1- 4: 22
Daya daga cikin shugabannin Ikklisiya mutum ne mai suna Istifanus. Yana da suna mai kyau yana kuma cike da Ruhu Mai Tsarki da hikima. Istifanus ya yi mu'ijizai yana kuma rinjayar hankulan mutane su gaskanta da Yesu.
Wata rana, sa'anda Istifanus yake koyarwa akan Yesu, wassu Yahudawa da basu gaskanta da Yesu ba suka fara jayayya da Istifanus. Suka hussata kwarai, suka yi karya akan Istifanus wa shugabannin addini. Suka ce, "Mun ji shi yana fadar mugayen abubuwa a kan Musa da Allah!" Saboda haka sai shugabanin addini suka kama Istifanus suka kai shi gaban babban firist da wasu shugabannin Yahudawa, inda ma su shaidar karya suka karu akan Istifanus.
Babban Firist din ya tambayi Istifanus, "Wannan abubuwan gaskiya ne?" Istifanus ya amsa da tunatar masu da manyan al'amuran da Allah ya yi daga zamanin Ibrahim zuwa zamanin Yesu, da yadda mutanen Allah suka ci gaba da yi masa rashin biyayya. Sai ya ce, "Ku kangararru, mutane masu tawaye, kullum kuna kin Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda kakannin ku, suka ki Allah suka kuma kashe annbawansa. Amma ku kun yi abin da yafi na su muni! Kun kashe Almasihu!"
Da shugabanin addinin suka ji haka, sai suka husata kwarai, suka toshe kunnuwan su suna ihu da karfi, suka ja Istifanus suka fitar da shi daga garin, suka jejjefe shi da duwatsu domin su kashe shi.
Sa'anda Istifanus ke mutuwa, sai ya yi kuka, "Yesu, ka karbi ruhu na," Sa'annan ya fadi da gwiwar sa, ya kara ihu, "Ubangiji, kada ka kama su da wannan laifin." Sa'an nan ya mutu.
Wani matashi mai suna Shawulu, ya amince da mutanen da suka kashe Istifanus ya kuma lura da rigunansu a lokacin da suke jifarsa da duwatsu. A wannan ranar mutane da yawa da ke zama a Urushalima suka fara tsananta wa masu bin Yesu, saboda haka masu bi suka gudu zuwa wassu wurare. Amma duk da haka kowane wuri suka je suna ta wa'azin Yesu.
Wani almajirin Yesu mai suna Filibus, daya ne daga cikin masu bi da suka gudu daga Urushalima a lokacin tsanani. Ya je Samariya inda ya yi wa'azin Yesu, mutane da yawa suka sami ceto. Wata rana wani mala'ika daga Allah ya ce wa Filibus ya je wani hanya a cikin hamada. Sa'adda yake tafiya a kan hanyar, Filibus ya ga wani jami'in Habasha mai daraja yana tafiya a cikin karusarsa. Ruhu Mai Tsarki ya gaya wa Filibus ya je ya yi wa mutumin magana.
Da Filibus ya zo kusa da Karusar, sai ya ji Bahabashen yana karatu daga littafin da annabi Ishaya ya rubuta. Mutumin yana karatu, ''Suka tafi da shi kamar dan rago don a kashe shi, kuma kamar yadda dan rago yake shiru, bai fadi ko kalma guda ba. Suka yi masa rashin adalci, ba su girmama shi ba. Suka dauke masa ransa daga gare shi."
Filibus ya tambayi Bahabashen, "Ko ka gane abinda kake karantawa?" Bahabashen ya amsa, "A'a, bazan iya ganewa ba sai dai idan wani ya bayyana mani. Ina rokon ka, ka shigo ka zauna kusa da ni. Ishaya yana rubutun nan game da kansa ne ko wani?"
Filibus ya bayyana wa Bahabashen cewa Ishaya yana rubutu ne akan Yesu, Filibus ya yi amfani da wadansu nassoshi domin ya gaya masa labari mai dadi akan Yesu.
Yayin da Filibus da Bahabashen suke tafiya, sai suka iso wani ruwa. Bahabashen ya ce, "Duba! ga ruwa nan! Ko za a yi mani baftisma?" Sai ya gaya wa matukin ya tsayar da karusar.
Sai suka gangara cikin ruwan, sa'annan Filibus ya yi wa Bahabashen baftisma. Bayan da suka fito daga cikin ruwan, sai nandanan Ruhu Mai Tsarki ya dauki Filibus zuwa wani wuri inda ya ci gaba da gaya wa mutane game da Yesu.
Bahabashen ya ci gaba da tafiyar sa zuwa gida, yana murna cewa ya san Yesu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Ayyukan Manzanni 6:8-8:5; 8:26-40
Shawulu ne saurayin da yayi tsaron tufafin mutanen da suka kashe Istifanus. Bai gaskanta da Yesu ba, saboda haka ya tsananta wa masu bi. Yana bi gida gida a Urushalima, domin ya kama maza da mata ya jefa su a kurkuku. Baban firist ya ba wa Shawulu izini ya je birnin Dimashku ya kama masu bi a can, ya dawo da su Urushalima.
Yayinda Shawulu ya ke kan hanyarsa zuwa Dimashku, sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi, sai ya fadi kasa, Shawulu ya ji wani ya ce, ''Shawulu, Shawulu me yasa kake tsananta mani?" Shawulu ya tambaya. "Wanene kai Ubangiji?" Yesu ya amsa masa "Ni ne Yesu. Kana tsananta mani!''
Da Shawulu ya tashi, bai iya gani ba, Sai da abokan sa suka bishe shi zuwa cikin Dimashku. Shawulu bai ci ko ya sha ba, har kwana uku.
Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya, Allah ya ce masa, "Ka je gidan da Shawulu ya ke zama, ka dibiya hannun ka a kansa domin ya sami gani kuma." Amma Hananiya ya ce, Ubangiji, na ji yadda mutumin nan yake tsananta wa masu bi. Allah ya amsa masa, ''Jeka! Na zabe shi domin ya yi shelar suna na ga Yahudawa da kuma wadansu mutane na wassu kabilu. Zai sha wahala masu yawa domin suna na.''
Sa'annan Hananiya ya tafi wurin Shawulu ya dibiya hannun sa akan sa, ya ce, "Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a hanyar ka zuwa nan, ya aike ni wurin ka domin ka sami gani ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki." Nandanan Shawulu ya iya gani kuma, Hananiya ya yi masa baftisma. Sai Shawulu ya ci abinci, sai karfin sa ya komo.
Nandanan, Shawulu ya fara yi wa Yahudawa da ke Dimashku wa'azi, cewa, "Yesu shine Dan Allah!" Yahudawa suka yi mamaki suna cewa mutumin da ya yi kokari ya hallakar da masu bi shi ma yanzu ya bada gaskiya ga Yesu! Shawulu ya ci gaba da ba da hujjoji masu kyau wa Yahudawa, da suke nuna cewa Yesu shine Almasihu.
Bayan kwanaki da yawa, Yahudawa suka yi shiri domin su kashe Shawulu. Suka aiki mutane su yi fakon sa a kofofin birnin domin su kashe shi. Amma Shawulu ya sami labarin wannan shiri, sai abokan sa suka taimake shi ya tsere. Wani dare suka saukar da shi ta bisan ganuwar birnin a cikin kwando. Bayan Shawulu ya tsere daga Dimashku, ya ci gaba da wa'azi akan Yesu.
Shawulu ya tafi Urushalima domin ya sadu da almajiran, amma suka ji tsoron sa. Sa'annan wani mai bin Almasihu mai suna Barnabas ya dauki Shawulu ya kai shi wurin manzannin, ya gaya masu yadda Shawulu ya yi wa'azi da gabagadi a Dimashku. Bayan wannan, almajiran suka karbi Shawulu.
Wadansu masu bi da suka tsere wa tsanani a Urushalima, suka tafi da nisa zuwa birnin Antakiya, suka kuma yi wa'azi akan Yesu. Yawancin mutanen da suke a Antakiya ba Yahudawa ba ne, amma da farkon nan yawancin su suka zama masu bada gaskiya. Shawulu da Barnabas suka tafi can su kara koyar wa sabobbin masu bada gaskiya game da Yesu su kuma karfafa Ikkilisiya. A garin Antakiya ne aka fara kiran masu bi "Kiristoci."
Wata rana, sa'anda Kiristoci a Antakiya suna azumi da addua, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce masu, "Ku kebe mani Barnabas da Shawulu domin aikin da na rigaya na kira su su yi" Sai Ikkilisiya da ke Antakiya ta yi wa Barnabas da Shawulu addu'a suka dibiya hannuwa a kansu. Sa'anan suka aike su, su je su yi wa'azin labari mai dadi akan Yesu a wurare da yawa. Barnabas da Shawulu suka koyar da mutane daga kabilu dabam dabam, mutane da yawa kuma suka ba da gaskiya ga Yesu.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Ayyukan Manzanni 8:3,9:1-31,11:19-26; 13:1-3
Yayin da Shawulu yayi tafiya cikin Gundumar mulkin Roma, sai ya fara amfani da sunansa na Romawa wato, "Bulus." Wata rana, Bulus da abokinsa Sila suka tafi garin Filifi, su yi wa'azin labarin nan mai dadi game da Yesu. Suka tafi wani wuri kusa da rafi waje da birnin, inda mutane ke taruwa su yi addu'a. Anan suka sadu da wata mace mai suna Lidiya, ita kuwa dillaliya ce. Tana kaunar Allah, tana kuma yi masa sujada.
Allah ya bude zuciyar Lidiya don ta gaskanta sakon nan game da Yesu, ita da iyalin gidanta kuma aka yi masu baftisma. Sai ta gayyaci Bulus da Sila su zauna a gidanta, su kuwa suka zauna tare da ita da iyalin ta.
Bulus da Sila sukan hadu da mutane a wurin addu'a. Kowace rana in suna tafiya can, wata yarinya baiwa da aljannu suka shige ta, tana bin su. Ta dalilin aljannun nan, takan fadi gaibu wa mutane. Ta haka ne ta kan samo wa iyayengijinta kudi da yawa ta wurin yin duba.
Baiwa yarinyar nan ta ci gaba da tada murya sa'adda suke tafiya, tana cewa, "Wadannan mutane bayin Allah Madaukaki. Suna fada maku hanyar da za ku bi ku tsira!" Ta yi haka akai akai, har Bulus ya ji haushi.
A karshe dai, wata rana da yarinya baiwan nan ta fara tada murya, Bulus ya juya wurinta ya ce wa aljannin da ke cikinta, "A cikin sunan Yesu, fita daga cikinta." Nan take aljannin ya rabu da ita.
Mutanen da suka mallaki yarinya baiwar suka yi hushi sosai! Sun gane da cewa in ba tare da aljannin ba, yarinya baiwar ba za ta iya fada wa mutane gaibu ba. Wannan na nufin cewa mutane ba za su kara biyan iyayengijinta kudi don ta fada wa mutanen gaibu ba.
Sai masu yarinya baiwa suka kai Bulus da Sila ga hukuman Romawa, su kuma suka doddoke su, suka kuma jefa su a kurkuku.
Suka sa Bulus da Sila a bangaren kurkukun da akwai tsaro sosai, har suka kafafunsu a turu. Duk da haka, a tsakiyar dare, suna raira wakokin yabo ga Allah.
Nandanan, sai ga girgizan kasa mai tsanani! Sai duk kofofin kurkukun suka bude, sarkokin 'yan yarin kuwa suka kwakkwance.
Mai tsaron kurkukun ya farka, da ganin kofofin kurkukun a bude, ya firgita! A tunaninsa duk 'yan sarkan sun tsere, sai yayi niyyar kashe kansa. (Ya sani cewa hukuman Romawa zasu kashe shi idan ya bar 'yan sarkan nan sun tsere.) Amma da Bulus ya gan shi, ya tada murya ya ce , "Dakata! Kada ka yi wa kan ka rauni. Dukkanmu muna nan."
Da rawanr jiki, mai tsaron kurkukun ya zo wurin Bulus da Sila yayi tambaya, "Me zan yi domin in sami ceto?" Bulus ya amsa, "Ka gaskanta da Yesu, Ubangiji, da kai da iyalinka zaku sami ceto." Sa'annan mai tsaron kurkukun ya dauki Bulus da Sila zuwa gidansa ya wanke raunukansu. Bulus yayi wa'azin labari mai dadi game da Yesu ga kowawanne dake gidansa.
Mai tsaron kurkukun da iyalinsa duka suka gaskanta da Yesu, aka kuma yi masu baftisma. Sa'annan mai tsaron kurkukun ya ba Bulus da Sila abinci, suka kuma yi farinciki tare.
Kashe-gari shugabannin birnin suka saki Bulus da Sila daga kurkuku, suka ce masu su fita daga Filibi. Bulus da Sila suka ziyarci Lidiya da wassu abokai kuma, sa'annan suka bar birnin. Labari mai dadin nan akan Yesu ya ci gaba da yaduwa, sannan Ikklisiya kuma ta ci gaba da girma.
Bulus da sauran shugabannin masu bi suka zaga birane da yawa, suna wa'azi suna koyar da labari mai dadi akan Yesu. Suka kuma rubuto wasiku da yawa don su karfafa, su kuma koyar da masubi a Ikklisiyoyi. Wassu daga cikin wasikun nan ne suka zama littattafai na Littafi Mai Tsarki.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Ayyukkan Manzanni 16:11-40
Sa'anda Allah ya hallici duniya, kome na da kyau. Babu zunubi. Adamu da Hauwa'u na kaunar juna, kuma suna kaunar Allah. Babu cuta ko mutuwa. Hakkan nan Allah yake so duniya ta kasance.
Shaitan yayi magana tawurin macijin acikin gonar domin ya rudi Hauwa'u. Sai ita da Adamu suka yi wa Allah zunubi. Domin sun yi zunubi, kowa aduniya yana rashin lafiya kuma kowa na mutuwa.
Saboda Adamu da Hauwa'u sun yi zunubi, wani abin da ya fi wannan muni ya faru. Suka zama makiyan Allah. Sakamakon haka, tun daga lokacin nan kowane mutum an haife shi da dabi'ar zunubi kuma ya zama makiyin Allah. Dangantaka tsakanin Allah da mutane ta yanke saboda zunubi. Amma Allah yana da shirin maido da wannan dangantakar.
Allah yayi alkawari cewa daya daga cikin zuriyar Hauwa'u zai murkushe kan shaidan, shaidan kuwa zai yi wa diddigen sa rauni. Wannan na nufin shaidan zai kashe Almasihu, amma Allah zai tada shi da rai kuma, sa'annan Almasihu zai murkushe ikon shaidan har abada. Bayan shekaru da yawa, Allah ya bayyana cewa Yesu shine Almasihu.
Sa'anda Allah ya hallaka dukkan duniya da ruwan tsufana, ya yi tanadin jirgi domin ya ceci mutanen da suka bada gaskiya a gareshi. Hakannan kuma, kowa ya cancanci hallaka saboda zunubansa, amma Allah ya yi tanadin Yesu ya cece kowa dake bada gaskiya gareshi.
Darurruwan shekaru, Firistoci suna ci gaba da mika hadayu ga Allah saboda mutane domin su nuna irin hukuncin da ya cancanci zunubansu. Amma wadannan hadayu basu iya kawar da zunubansu ba. Yesu shine Babban Firist Mafi Girma. Ba kamar sauran firistoci ba, ya mika kansa a matsayin muhimmin hadaya da zai kawar da zunubi na dukkan mutanen duniya. Yesu shine cikakken Babban Firist saboda ya dauki hukunci na kowane zunubi da kowa ya taba aikatawa.
Allah yace wa Ibrahim, "Dukkan kabilu na mutanen duniya zasu sami albarka ta wurin ka." Yesu zuriyan Ibrahim ne. Dukkan kabilu na mutane sun sami albarka ta wurinsa, saboda duk wanda ya gaskanta da Yesu ya sami ceto daga zunubi, ya kuma zama zuriyar Ibrahim ta ruhaniya.
Sa'anda Allah yace wa Ibrahim ya mika dansa, Ishaku, a matsayin hadaya, Allah ya tanada rago domin hadayar amaimakon dansa, Ishaku. Dukkan mu mun cancanci mutuwa domin zunubanmu! Amma Allah ya tanada Yesu, 'Dan Ragon Allah, a matsayin hadaya, don ya mutu a madadinmu.
Sa'anda Allah ya aiko da annoba ta karshe a Masar, yace wa kowane iyalin Isra'ila su yanka rago marar aibi su watsa jinin a sama da gefen kofofinsu. Sa'anda Allah ya ga jinin, ya ketare gidajensu kuma bai kashe yayan farin su ba. Wannan alamari ana kiransa Ketarewa.
Yesu shine 'Dan Rago Ketarewar mu. Shi cikakke ne kuma marar zunubi, aka kuma kashe shi a lokacin idin Ketarewa. Sa'adda duk wani mutum ya gaskanta da Yesu, jinin Yesu ya biya hakin zunubin mutumin, kuma hukucin Allah ya ketare wannan mutum.
Allah ya yi alkawari da Isra'ilawa, wadanda sune zababbun mutanensa. Amma yanzu Allah ya yi sabon alkawari dake iya samuwa ga kowa. Saboda wannan sabon alkawari, kowane mutum daga kowane kabilun mutane zai iya zama daga cikin mutanen Allah ta wurin bada gaskiya ga Yesu.
Musa babban annabi ne wanda yayi shelar maganar Allah. Amma Yesu ne mafificin annabi na dukka. Shi Allah ne, saboda dukkan abinda ya yi ko ya fada, ayyukane da kuma kalmomin Allah. Don hakka aka ce da Yesu Kalmar Allah.
Allah yayi wa Sarki Dauda alkawari cewa daya daga zuriyar sa zai yi mulki a akan mutanen Allah a matsayin sarki har abada. Saboda Yesu Dan Allah ne kuma Almasihu, shine wannan kebabben zuriyar Dauda wanda zai iya mulki har abada.
Dauda sarkin Isra'ila ne, amma Yesu sarki ne na duniya gabaki daya! Zai sake dawowa yayi mulki da adalci da kuma salama, har abada.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 1-3,6; 14, 22, Fitowa 12, 20; 2 Sama'ila 7; Ibraniyawa 3:1-6, 4:14-5:10, 7:1-8:13, 9:11-10:18; Wahayin Yahaya 21
Wani mala'ika ya ce wa wata budurwa wanda ake ce da ita Maryamu, zata haifi Dan Allah.Tun tana budurwa Ruhu Mai Tsarki ya lullube ta, ta kuma yi ciki. Ta haifi da ta kuma sa masa suna Yesu. Domin haka, Yesu Allah ne kuma mutum.
Yesu yayi al'ajibai da yawa da suka bada tabbatarwa shi Allah ne. Yayi tafiya akan ruwa, ya lafar da ruwan sama mai iska, ya warkar da mutane marasa lafiya da yawa, ya kori aljannu, ya tada matattu zuwa rai, ya juya dunkulen gurasa biyar da kifi biyu zuwa issashen abinci domin mutane fiye da 5,000.
Yesu kuma babban mallami ne, ya kuma yi magana da iko saboda shi Dan Allah ne. Ya koyar cewa, ya kamata ka kaunaci sauran mutane kamar yadda kake kaunar kanka.
Ya kuma koyar cewa, ya kamata ka kaunaci Allah fiya da yadda zaka kaunaci sauran abubuwa, harma da dukiyar ka.
Yesu yace, mulkin Allah yafi komai a duniya daraja. Abu mafi muhimmanci ga kowa shine ya kasance a mulkin Allah. Idan zaka shiga mulkin Allah, dole ne a cece ka daga zunuban ka.
Yesu ya koyar cewa wadansu mutane zasu karbe shi su kuma sami ceto, amma wadansu ba zasu karba ba. Ya ce wadansu mutane suna kama da kasa mai kyau. Sun karbi labari mai dadi na Yesu kuma suka sami ceto. Wadansu mutane suna kama da kasa mai tauri dake kan hanya, inda irin maganar Allah ba ya shiga, kuma basa ba da wani amfani. Wadannan mutanen sukan ki sako game da Yesu kuma baza su shiga mulkinsa ba.
Yesu ya koyar da cewa, Allah yana kaunar masu zunubi kwarai. Yana so ya gafarta masu, ya kuma maishe su 'ya'yansa.
Yesu kuma ya gaya mana ce wa Allah ya tsani zunubi. Sa'anda da Adamu da Hauwa'u suka yi zunubi, ya shafi dukkan zuriyar su. Sakamakon haka, kowane mutum a duniya ya yi zunubi, a rabe kuma ya ke da Allah. Domin haka, kowa ya zama abokin gaba na Allah.
Amma Allah ya kaunaci kowa a duniya sosai harma ya bada makadaicin dansa, domin duk wanda ya ba da gaskiya ga Yesu ba za a hukunta shi saboda zunubansa ba, amma zai kasance tare da Allah har abada.
Saboda zunubinka, kayi laifi kuma ka cancanci mutuwa. Ya kamata Allah yayi fushi da kai, amma ya zuba fushinsa akan Yesu amaimakonka. Sa'adda Yesu ya mutu akan giciye, ya karbi hukuncinka.
Yesu bai taba yin zunubi ba, amma ya zabi a hukuntashi, kuma ya mutu a matsayin hadaya cikakkiya domin ya kawar da zunubanka da zunuban kowanne mutum a duniya. Saboda Yesu ya mika kansa hadaya, Allah zai iya gafarta kowanne zunubi, har ma da munanan zunubai.
Ayyuka nagari ba zasu cece ka ba, Babu abinda za ka iya yi ka sami dangantaka da Allah. Yesu ne kadai zai iya wanke zunubanka. Dole ne ka gaskanta Yesu Dan Allah ne, ya kuma mutu akan gicciye maimakon ka, Allah ya kuma tashe shi da rai.
Allah zai cece duk wanda ya bada gaskiya ga Yesu, ya kuma karbe shi a matsayin Ubangijinsu. Amma ba zai ceci ko dayan da bai ba da gaskiya gare shi ba. Ba ya zabi ko kai mai arzikine ko talaka, na miji ko ta mace, tsoho ko matashi, ko inda kake zama. Allah yana kaunar ka kuma yana so ka bada gaskiya ga Yesu domin ya sami dangantaka na kusa da kusa.
Yesu na gaiyatarka ka bada gaskiya gare shi kuma ayi maka baftisma. Ka bada gaskiya Yesu shine Almasihu, makadaicin Dan Allah? Ka bada gaskiya kai mai zunubi ne kuma ka cancanci Allah ya hukunta ka? Ka gaskanta Yesu ya mutu akan gicciye domin ya dauke zunubanka?
Idan ka bada gaskiya ga Yesu da abinda yayi maka, kai Krista ne! Allah ya fitar da kai daga mulkin Shaidan ta duhu, kuma ya saka cikin Mulkin Allah na haske. Allah ya dauke tsofofin hanyoyin yin zunubin ka, ya kuma baka sabobin hanyoyin yin adalci.
Idan kai Kirista ne, Allah ya gafarta zunubanka saboda abinda Yesu ya yi. Yanzu, Allah na ganin ka a matsayin abokin sa na kusa a maimakon makiyi.
Idan kai abokin Allah ne da kuma bawan Yesu Ubangiji, za ka so kayi biyayya da abinda Yesu yake koya maka. Ko da shike kai Krista ne, za'a iya jarabtar ka yi zunubi. Amma Allah mai aminci ne kuma yace idan ka furta zunubanka, zai yafe maka. Zai baka karfi kayi yaki da zunubi.
Allah yace kayi addu'a, kayi nazarin maganarsa, ka bauta masa tare da sauran Kiristoci, ka kuma gaya wa wadansu abinda ya yi maka. Dukkan wadannan abubuwa za su taimake ka wurin samun dangantaka mai zurfi da shi.
Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Romawa 3:21-26, 5:1-11; Yahaya 3:16; Markus 16:16; Kolosiyawa 1:13-14; 2 Korantiyawa 5:17-21; 1 Yahaya 1:5-10
Kusan shekaru 2000, kari bisa kari na mutane a duniya suna sauraron labari mai dadin nan game Yesu wanda Almasihun. Ikklisiya ta na ta girma. Yesu ya yi alkawari zai dawo a karshen duniya. Ko da yake bai dawo ba tukuna, zai cika alkawarinsa.
Yayin da muke jiran dawowar Yesu, Allah yana so muyi rayuwar a hanya ta tsarki da ke girmama shi. Yana kuma so mu fada wa wadansu game da mulkin sa. Lokacin da Yesu ke rayuwa a duniya, ya ce, "Almajiraina za su yi wa'azin labari mai dadin nan game da mulkin Allah ga mutane ko'ina a duniya, sa'annan karshe zai zo."
Kabilun mutane da yawa har yanzu basu ji labarin Yesu ba. Kafin tafiyar sa sama, Yesu ya fada wa Kiristoci su yi wa'azin labari mai dadin nan ga mutanen da ba su taba ji ba. Ya ce, "Ku je ku almajirantar da dukkan kabilun mutane!" kuma, "Filaye sun nuna domin girbi!"
Yesu ya kuma ce, "Bara dai, bai fi maigidansa girma ba. Kamar yadda hukumomin duniyan nan suka ki ni, za su azabtar da ku, su kuma kashe ku saboda ni. Ko da yake a wannan duniya za ku sha wahala, ku sami karfafawa domin Na yi nasara da Shaidan, wanda ke mulkin duniyan nan. Idan kuka ci gaba da aminci da ni har zuwa karshe, Allah zai cece ku!''
Yesu ya fada wa almajiransa wani labari wanda zai bayyana abin da zai faru da mutane a lokacin da duniya ta kai ga karshe. Ya ce, "Wani mutum ya shuka iri mai kyau a filinsa. Sa'anda ya ke barci, makiyin sa ya zo ya shuka wuta-wuta tare da alkamar, sai ya tafi abinsa."
"Sa'anda da shukan suka fito, barorin mutumin suka ce, 'Maigida, ka shuka iri mai kyau a filin can. Me ya sa akwai wuta-wuta a ciki?' Maigidan ya amsa, 'Wani makiyi ne lallai ya shuka su."'
''Barorin sun amsa wa maigidansu suka ce, 'Ko mu tuge wuta-wutan ne?' Maigidan ya ce, 'A'a. Idan kuka yi haka, za ku tuge wassu alkama tare da su. Ku dakata zuwa lokacin girbi sa'annan za ku tara wuta-wutan dami dami a kone su, amma ku kawo alkamar a cikin rumbu na.'''
Almajiran ba su gane ma'anar labarin ba, sai suka roki Yesu ya bayyana masu. Yesu ya ce, "Mutumin da ya shuka iri mai kyau, yana a madadin Almasihu. Filin kuma, a madadin duniya. Iri mai kyau kuma, a madadin mutane na mulkin Allah."
"Wuta-wutan kuma, a madadin mutanen da ke na mugun. Makiyin nan da ya shuka wuta-wuta kuma, a madadin iblis. Girbin kuma, a madadin karshen duniya, masu yin girbin kuma, a madadin mala'ikun Allah."
"Lokacin da duniya ta zo karshe, mala'iku za su tattara dukan mutane da ke na iblis, su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa, inda za su yi kuka da cizon hakora a cikin azaba mai tsanani. Sa'annan adalai za su haskaka kamar rana cikin mulkin Allah Ubansu."
Yesu kuma ya ce zai dawo duniya, kafin duniyar ta zo ga karshe. Zai dawo kamar yadda ya tafi, wannan na nufin, zai kasance cikin jiki, zai zo bisa gajimare na sararin sama. Lokacin da Yesu zai dawo, duk Kiristan da ya mutu zai tashi daga matattu ya same shi a sararin sama.
Sa'annan Kiristocin da ke a raye har yanzu kuma za su tashi zuwa cikin sararin sama, su hadu da sauran Kiristoci da suka tashi daga matattu. A can, dukkansu za su kasance tare da Yesu. Bayan haka, Yesu zai zauna tare da mutanensa cikin cikakkiyar salama da dayantaka na har abada.
Yesu ya yi alkawari zai ba da rawani ga dukkan wadanda suka gaskanta da shi. Za su yi rayuwa, su kuma yi mulki tare da Allah cikin cikakkiyar salama na har abada.
Amma Allah zai shar'anta dukkan wanda bai bada gaskiya ga Yesu ba. Zai jefa su cikin jahannama, inda za su yi kuka da cizon hakora cikin kunci na har abada. Wutan da ba ta mutuwa, za ta ci gaba da kona su, tsutsotsi kuma ba za su daina cin su ba.
Lokacin da Yesu zai dawo, zai hallaka Shaidan gaba daya da mulkin sa. Zai jefa Shaidan cikin jahannama inda zai kone har abada, tare da duk wanda ya zaba ya bi shi, a maimakon yin biyayya ga Allah.
Domin Adamu da Hauwa'u sun yi wa Allah rashin biyayya, sun kuma kawo zunubi a wannan duniya, Allah ya la'anta ta, ya kuma yanke shawara ya hallaka ta. Amma wata rana, Allah zai hallici sabuwar sama da sabuwar duniya da za ta zama cikakkiya.
Yesu da mutanensa za su zauna a sabuwar duniyar, kuma zai yi mulki na har abada bisa dukkan kome da ya kasance. Zai share dukkan hawaye, kuma ba za a kara samun wahala, bakin ciki, kuka, mugunta, ciwo, ko mutuwa ba. Yesu zai yi sarautar mulkin sa da salama da adalci, zai kuma kasance tare da mutanensa har abada.
Labarin a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 24:14; 28:18; Yahaya 15:20, 16:33; Wahayin Yahaya 2:10; Matta 13:24-30, 36-42; 1Tassalonikawa 4:13-5:11; Yakubu 1:12; Matta 22:13; Wahayin Yahaya 20:10, 21:1-22:21
Gayyata!
Muna so mu watsa wannan ƙarami Littafi Mai Tsarki cikin _kowane harshe cikin duniya _ kuma kuna iya taimakonmu! Aikin mai yiyuwa ne--muna tunnani zai faru idan dukan jikin Kiristi yana aiki tare don fasara da rarraba albarkun.
Rabawa hannu sake
Raba wannan albarkun kamar yadda ku ke so ba fasawa. Duka na cikin na'ura kyautai ne bisa internet, kuma domin lisans abuɗe take don amfani, kuna iya sake buga Labarun Littafi Mai Tsarki (Open Bible Stories) don saidawa ko'ina cikin duniya ba za ku biya kuɗin kamasho. Samu ƙarin bayani a http://openbiblestories.org.
Ƙarawa!
Samu Labarun Littafin Mai Tsarki (Open Bible Stories) kamar funafune da aɓli selula cikin waɗansu harsuna a http://openbiblestories.org. Bisa hanyoyi saduwa da na'ura kuna iya samu taimako fasarar Labarun Littafin Mai Tsarki cikin harshenku.